Ziyarar gwamonin APC ga Goodluck Jonathan: PDP ta yi martani

Ziyarar gwamonin APC ga Goodluck Jonathan: PDP ta yi martani

- Ziyarar da gwamnonin APC suka kaiwa tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan na ci gaba da haifar da cece-kuce

- PDP a martaninta ga ziyarar na gwamnonin APC ta bayyana shi a matsayin lamuncewa adawa

- Kakakin jam’iyyar, Ologbondiyan ya ce ziyarar ya kuma tabbatar da cewar Najeriya ta fi inganta a karkashin shugabancin PDP

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana cewa ziyarar da gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) suka kaiwa tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kara tabbatar da cewar Najeriya ta fi inganta a karkashin mulkinta.

Legit.ng ta tattaro cewa PDP ta bayyana hakan ne yayinda take martani ga ziyarar da gwamnan suka kai a ranar Juma’a, 20 ga watan Nuwamba, inda ta bayyana hakan a matsayin lamuncewa mulkin jam’iyyar adawar.

Gwamnonin APC karkashin jagorancin Shugaban jam’iyyar kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni sun gudanar da wani taron sirri tare da Jonathan a gidansa da ke Abuja.

Ziyarar gwamonin APC ga Goodlucki Jonathan: PDP ta yi martani
Ziyarar gwamonin APC ga Goodlucki Jonathan: PDP ta yi martani Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: An kama wasu mutane biyu da suka yi wa dan sanda gashin tsire tare da cin namansa

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, 22 ga watan Nuwamba, ta kakakinta, Kola Ologbondiyan.

A cewar Ologbodinyan, jam’iyyar adawar ta amshi ziyarar na gwamnonin APC a matsayin ban hakuri daga jam’iyya mai mulki zuwa PDP da yan Najeriya a kan karairayi da sauran zarge-zarge da aka yi amfani da su don karbar mulki.

Ologbodiyan ya kuma gargadi yan Najeriya a kan su yi taka-tsantsan da dabarun APC, cewa jam’iyyar ba za ta bari gajiyayyar jam’iyyar da makiranta su sake batar dasu ba.

KU KARANTA KUMA: Dattijon arewa, Kwande, ya bayyana dalilin da zai sa shugaban kasa ya sake fitowa daga yankin

A gefe guda, wani rahoto ya yi ikirarin cewa jam’iyyar APC na zawarcin tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan, domin ya fito takarar Shugaban kasa a inuwarta a 2023.

Rahoton wanda jaridar This Day ta kawo ya yi ikirarin cewa wasu shugabannin jam’iyyar na matsawa tspohon Shugaban kasar a kan ya duba yiwuwar amsa tayin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng