Sojoji sun daƙile harin ISWAP a Magumeri

Sojoji sun daƙile harin ISWAP a Magumeri

- Sojojin Najeriya sun dakile wata hari da 'yan ta'addan kungiyar ISWAP suka yi yunkurin kai wa a Magumeri

- 'Yan ta'addan sun yi yunkurin kai harin ne misalin karfe biyar na yamma kamar yadda rahoton ya bayyana

- Amma a halin yanzu rundunar sojojin Najeriya ba ta fitar da sanarwar game da yunkurin harin ba

Rundunar sojin Najeriya, a ranar Juma'a ta dakile lalata wani hari da mayakan ISWAP suka kai garin Magumeri, a Jihar Borno, Arewa maso gabashin Najeriya.

Karamar hukumar Magumeri, ta kai nisan kilo mita 50 daga Maiduguri babban birnin jihar Borno.

HumAngle ta ruwaito cewa harin ya afku da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Juma'a 20 ga watan Nuwamba.

Sojoji sun dakile harin ISWAP a Magumeri
Sojoji sun dakile harin ISWAP a Magumeri. Hoto daga Hum Angle
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Na gwammace a datse min kai a maimakon in bada haƙuri', martanin Bashir El Rufai ga masu sukar hotunansa da Nwakaego

Ba a samu cikaken bayanai game da harin ba har zuwa lokacin da aka hada wannan rahoto kuma rundunar soji ba tace komai ba akan lamarin ba.

Magumeri ta fuskanci hare haren ta'addanci a baya bayan nan akan jami'an tsaro da ragowar farar hula.

A 2019, sojoji suka sami nasarar kwato garin kasancewar umarnin gwamnati na kafa sansanin sojoji da kuma shawo kan matsalar tsaro a wasu garuruwa, ciki har da wani hari da aka kaiwa sojoji a watan Mayu a Magumeri.

KU KARANTA: 'Yan jam'iyyar APP 20,000 ciki da shugbansu sun koma PDP a Ebonyi

Sake girke jami'ain sojoji a Magumeri da kewaye yana da alaka da yadda ISWAP suka mamaye yankin da hare hare kan sojoji da al'umma.

Garin, yana da muhimmanci ga ISWAP wajen rarraba makamai da sauran kayyakin amfani ga sauran sassan da mayakanta su ke.

A watan Oktoba, an kashe mayaka da dama lokacin da ISWAP suka kai wami hari kan sansanin sojoji a Magumeri.

Ko a cikin watan Agusta, fiye da manoma da makiyaya 12 ne aka kashe tare da barnatar da dabbobi lokacin wani hari a Puciwa da Koleram dake karamar hukumar Magumeri.

A wani labarin, Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya siffanta Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin 'raɓa' a yayin da ya ke tsokaci a kan wani littafi da aka rubuta kan shugaban kasar mai taken "The Buhari in Us".

Yahaya Bello ya furta hakan ne cikin wani faifan bidiyo da ya bazu a shafunkan sada zumunta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164