Fashola ya bayyana dalilin da yasa ba'a kammala aikin titin Kano zuwa Kaduna da Abuja ba

Fashola ya bayyana dalilin da yasa ba'a kammala aikin titin Kano zuwa Kaduna da Abuja ba

- Ma su amfani da babban titin da ya tashi daga Kano zuwa Kaduna zuwa Abuja suna yawan korafi da samun jinkiri a hanya

- Ana samun jinkiri a hanyar ne saboda gyaran titin da ake yi, wanda aka fara kimanin shekaru uku da suka gabata

- Ministan aiyuka da gidaje, Babtunde Fashola, ya ce wata bukata da sanatoci suka nema ita ta haddasa jinkiri a aikin

Ministan ayyuka da da gidaje, Baba Tunde Fashola, ya bayyana irin ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ke yi don ganin ta ƙarasa kammala aikin sake titin da ya haɗa Kano, Kaduna da Abuja.

Ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki da ma'aikatar ayyuka da gidaje ta gudanar a Jami'ar jihar Kaduna (KASU), a ranar Alhamis.

Fashola yace; "Shugaban ƙasa ya nuna damuwarsa da kuma maida hankalinsa don ganin an kammala aikin kafin wa'adin mulkinsa ya ƙare".

Ya ce manufar wannan taron shine gano inda gizo yake saƙar da kuma bayanai akan ƙalubalen da suke tattare da aikin titin.

KARANTA: Janar Abubakar Sa'ad ya shigar da karar Buratai, ministan tsaro, da ilahirin rundunar soji

Da yake amsa tambayoyin da masu ruwa da tsaki suka yi masa a kan mai ya kawo tsaiko a aikin titin, Fashola ya ce babban dalilin da yasa ba'a fara aikin da wuri ba shine roƙon da majalisa tayi na neman a faɗaɗa titin daga hannu biyu zuwa hannu uku.

Fashola ya bayyana dalilin da yasa ba'a kammala aikin titin Kano zuwa Kaduna da Abuja ba
Fashola ya bayyana dalilin da yasa ba'a kammala aikin titin Kano zuwa Kaduna da Abuja ba
Asali: Facebook

A maganar da yayi, ya ce; "Jim kaɗan bayan mun fara aikin titin, mun karɓi wasiƙa daga majalisar ƙasa tana mai roƙon gwamnatin tarayya kan ta faɗaɗa titin maimakon hannu biyu zuwa uku.

"Ba daga mu bane, daga Sanatoci ne kuma sun aikewa shugaban ƙasa ni kuma sun bawa ma'aikata ta kwafin wasiƙar.

"Sakamakon umarnin da muka karɓa daga shugaban ƙasa akan a faɗaɗa tituna, muna buƙatar sake taswirar don samar da gurbin gadajoji daban daban har guda 40 a wannan titin don samar da hannaye uku.

"Saboda haka, idan har za'a faɗaɗa titin, dole sai an sake tsarashi, kuma ana buƙatar ɗauko hayar ƙwararre mai tsara-tsare da zane. Ya zama dole mu bi bukatar majalisar" a cewarsa.

KARANTA: A kama shi duk inda aka gan shi; umarnin kotu bayan janye belin Abdulrasheed Maina

Ya ce buƙatar da majalisar ta samar ba ƙarama bace kuma doguwa wadda take buƙatar tallatawa, bibiyar tsarin da kuma ɗauko ƙwarrarren masanin zane da tsara tituna.

"Sannan muna buƙatar sahalewar BPP (Bureau for Public Procurement) sai kuma na ƙarshe sahalewar gwamnatin tarayya (FEC) don ɗauko hayar ƙwararren masanin tsare tsare kamar yadda aka buƙata.

Ministan ayyuka da gidaje Baba Tunde Fashola ya bayyana cewa Shugaban ƙasa Muhammad yafi maida hankalinsa da nuna damuwar kammala titin Abuja zuwa Kaduna da Kano kafin cikar wa'adinsa.

Fashola ya bayyana cewa Shugaban ƙasa Muhammad ya fi maida hankalinsa da nuna damuwar kammala titin Abuja zuwa Kaduna da Kano kafin cikar wa'adinsa.a aikin da wuri ba.

Fashola yace akwai buƙatar ɗauƙo ƙwarren masanin tsare matuƙar ana son faɗaɗa titin zuwa hannaye uku kamar yadda majalisa ta buƙata,kuma suna buƙatar sahalewar hukumomi.

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa cewa; Rundunar 'yan sanda ta sanar da cewa ta kubutar da manyan 'yan sanda tara, dukkansu ASP, da aka sace tun ranar takwas ga watan Nuwamba na wannan shekarar a tsakanin jihar Katsina.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel