Kotu ta janye belin Abdulrasheed Maina, ta bada umarnin a kama shi

Kotu ta janye belin Abdulrasheed Maina, ta bada umarnin a kama shi

- Babbar kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a Abuja ta bukaci a kama Abdurasheed Maina a duk inda aka gan shi

- Sanata Ali Ndume, mai wakiltar jihar Borno ta kudu, ne ya karbi belin Maina a kan kudi miliyan N500

- Kafin Ndume ya karbi belinsa, Maina ya shafe watanni bakwai a gidan yarin Kuje da ke birnin tarayya, Abuja

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da umarnin janye belin Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban tawagar gyaran fanshon ma'aikata (PRTT) da gwamnati ta rushe.

A hukuncin da alkalin kotun, Okong Abang, ya zartar ranar Laraba, ya bayar da umarnin a sake kamo Maina ''duk inda aka gan shi".

Lauyan hukumar EFCC, Mohammed Abubakar, ya ce an bayar da belin Maina a kan kudi miliyan N500 da kuma mai tsaya masa; wanda dole ya kasance Sanata mai ci da zai ajiye miliyan N500 a kotu.

KARANTA: 'Yan bindiga sun sace ASP 12 daga tawagar 'yan sanda a tsakanin Katsina zuwa Zamfara

Lauyan ya rubuta takardar korafi zuwa kotun inda a ciki ya zargi Maina da saba sharuda da ka'idojin belin.

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci ta gurfanar da Maina a gaban kotu bisa tuhuma goma sha biyu da ta shirya a kansa da kuma wani kamfani mai suna 'Common Input Properties & Investment Limited".

Bayan bawa hukumomin tsaro izinin kama shi, kotun ta bawa EFCC damar gurfanar da shi tare da tuhumarsa a kebance.

Kotu ta janye belin Abdulrasheed Maina, ta bada umarnin a kama shi
Maina da Ndume
Asali: Twitter

Kazalika, kotun ta saka ranar 23 ga watan Nuwamba, domin bawa Sanata Ali Ndume, wanda ya tsayawa Maina, damar yin bayanin dalilin da zai hana shi rasa kudin beli N500m da ya bayar.

A cewar kotun, za'a saka kudin da Sanatan ya biya a aljihun gwamnatin tarayya saboda saba ka'ida da sharudan da aka bayar da Maina beli a kansu.

KARANTA: Batan tiriliyan uku da biliyan fiye da ashirin: Majalisa ta gayyaci Malam Kyari da Emefiele

Kotun ta dauki wannan mataki bayan ta gamsu da hujjar EFCC a kan cewa Maina ya ki halartar zaman kotu har sau hudu a jere ba tare da wani dalili mai kwari ba.

Kafin Sanata Ndume ya karbi belinsa, Maina ya shafe tsawon watanni bakwai a gidan yarin Kuje.

EFCC ta na zargin Maina da wawure kimanin biliyan biyu ta hanyar amfani da kamfanin ''Common Input Properties & Investment Limited".

A ranar Talata ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa birgediya janar (mai ritaya), Abubakar Sa'ad, ya shigar da karar ilahirin rundunar soji a gaban kotun ma'aikata (NIC) domin kalubalantar yi masa ritayar dole.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng