DSS ta tsare dogarin Gbajabiamila da ya kashe mai talan jarida a Abuja

DSS ta tsare dogarin Gbajabiamila da ya kashe mai talan jarida a Abuja

- Hukumar DSS ta ce ta tabbatar da cewa jami'inta ne ake zargi da kashe mai talan jarida, Ifeanyi Okereke a Abuja

- Hukumar ta DSS ta ce a matsayin matakin ladabtarwa ta tsare jami'in nata sannan ta fara gudanar da bincike

- Hukumar ta DSS ta ce za ta yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro da abin ya shafa wurin zurfafa bincike kan lamarin

Hukumar Yan Sandan Farin Kaya, SSS, ta tabbatar da cewa jami'inta da ke tsaron Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila ne ake zargi da kashe mai talan jarida, Ifeanyi Okereke a Abuja.

A cikin sanarwar da ta fitar ta bakin kakakinta Peter Afunanya, hukumar ta kuma ce jami'in a yanzu an tsare shi sannan an janye shi daga tawagar kakakin majalisar.

Da duminsa: DSS ta tsare dogarin Gbajabiamila da ya kashe mai talan jarida a Abuja
Da duminsa: DSS ta tsare dogarin Gbajabiamila da ya kashe mai talan jarida a Abuja. Hoto @daily_nigerian
Asali: UGC

DUBA WANNAN: 'Na gwammace a datse min kai a maimakon in bada haƙuri', martanin Bashir El Rufai ga masu sukar hotunansa da Nwakaego

"An janyo hankalin Hukumar Yan sandan Faran Hula, DSS, game da zargin harbi da kashe wani Ifeanyi Okereke da wani jami'in tsaro da ke tawagar kakakin majalisar wakilai na tarayya.

"Hukumar ta tabbatar cewa wanda ake zargin jami'inta ne kuma yana daya daga cikin 'yan tawagar kakakin majalisar. Kamar yadda kakakin majalisar ya fadi ya dakatar da shi daga tawagarsa kuma hukumar ta janye shi daga aiki tare da kakakin majalisar.

KU KARANTA: Wike ya ce wani gwamnan PDP daya zai sake fita daga jam'iyyar

"A cikin matakan ladabtarwa, an tsare shi a halin yanzu. Hukumar ta fara gudanar da sahihin bincike kan abinda ya faru. A yayin da ta yi alkawarin cewa ba za tayi rufa-rufa ba a yayin binciken, za ta yi aiki tare da hukumomin da abin ya shafa don yin binciken," a cewar Mista Afunanya cikin sanarwar da ya aike wa Daily Nigerian.

A wani labarin, an kama wata mata mai shekaru 40 da haihuwa mai suna Ruqayya Rabi'u a Jigawa bayan samun ta da jabun kuɗade (dubu ɗai-dai guda 100 da ɗari biyar-biyar guda 76) a ƙaramar hukumar Birnin Kudu.

Wacce ake zargin dai ƴar asalin ƙaramar hukumar Bichi ne a Kano ta shiga hannu ne bayan ta siya man shafawa na N300 a kasuwa kamar yadda LIB ya ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel