Mutane 24 sun gamu da fushin PDP, Jam’iyya ta dakatar da su a Jihar Ebonyi

Mutane 24 sun gamu da fushin PDP, Jam’iyya ta dakatar da su a Jihar Ebonyi

- A jihar Ebonyi, an dakatar da wasu mutane 24 daga Jam’iyyar PDP

- Daga cikinsu har da tsohon Gwamna - Sanata a yanzu, Sam Egwu

- Shugabannin PDP sun zargi ‘ya ‘yan na su da laifin yin zagon-kasa

A ranar Juma’a, 20 ga watan Nuwamba, 2020, jam’iyyar PDP ta reshen jihar Ebonyi, ta dakatar da wasu daga cikin ‘ya ‘yanta, Vanguard ta rahoto hakan.

Jaridar ta ce jam’iyyar hamayyar ta dakatar da ‘ya ‘yan na ta ne saboda zargin su da ake yi da yi wa jam’iyya zagon-kasa da kuma wasu laifuffuka masu girma.

Wadanda aka dakatar sun hada da tsohon gwamnan jihar, da kuma duka ‘yan majalisar tarayya masu ci da su ka fito daga Ebonyi, da kuma wasu kusoshin.

KU KARANTA: Gwamnonin Jihohi 3 sun shiga yarjejeniya da Jam’iyyar APC

Mutane 24 aka buga wa gudumar jam’iyyar kamar yadda aka bayyana bayan an tashi taron majalisar SWC da shugabannin PDP na reshen Ebonyi su yi.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi wannan muhimmin zama ne ranar Alhamis a garin Abakaliki.

Jam’iyyar PDP da ta zama mai adawa a Ebonyi ta fitar da jawabi ne ta bakin shugabanta da sakataren labarai, Onyekachi Nwebonyi da Simon Anyigor.

Barista Onyekachi Nwebonyi da Cif Simon Anyigor su ka ce wadanda dakatarwar ta shafa za su bayyana gaban kwamitin ladabtar wa domin kare kawunansu.

Mutane 24 sun gamu da fushin PDP, Jam’iyya ta dakatar da su Jihar Ebonyi
PDP ta dakatar da Sam Egwu Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: An nemi a bani Minista sau 3 amma na ce a kai kasuwa – Gbagi

“Wadanda aka dakatar sun hada da Sanatoci masu-ci, Michael Ama Nnachi da Obinna Ogba, Honarabul. Chukwuma Nwazunku, da kuma Sylvester Ogbaga."

Ragowar wadanda matakin ya shafa su ne: Hon. Livinus Makwe, Hon. Chris Usulor, Hon. Victor Aleke da tsohon gwamna Sanata Sam Egwu, da wasu mutane 16.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel