Karin albashin Malamai: Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da kwamitin aiwatarwa

Karin albashin Malamai: Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da kwamitin aiwatarwa

- A kwanakin baya ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya sanar da yi wa malaman makaranta karin albashi na musamman

- Sai dai, gwamnatocin jihohi sun yi watsi da batun tare da sanar da cewa ba zasu iya kaddamar da tsarin ba

- Yanzu haka gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta kafa kwamitin da zai bullo da hanyar tabbatar da sabon tsarin

Gwamnatin tarayya, a ranar Alhamis, ta ƙaddamar da kwamiti don ƙirƙiro hanyoyin da za'a bi don cimma gyarawa malamai masu koyarwa a makarantun sakandire albashinsu.

Wannan cigaban ya zo ne bayan alwashi da romon baka da Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yiwa malamai lokacin bikin murnar Ranar Malamai ta duniya a birnin tarayya Abuja.

Ministan Ilimi, Mallam Adamu Adamu, da yake magana akan taron da aka gudanar a ofishinsa, ya ce; "kwamitin aiwatarwa na ƙasa me bibiya da gyara akan harkar koyarwa a Najeriya an kafa shine don inganta koyo da koyarwa a faɗin ƙasar nan."

Kwamitin wadda babban sakataren ma'aikatar ilimi, Arc. Sonny Echono, ke shugabanta, ya rabu zuwa ƙananan kwamitoci 12 don mayar da hankali akan muhimman ɓangarori na musamman da suke buƙatar sa hannu da tallafawa.

KARANTA: Kotu ta janye belin Abdulrasheed Maina, ta bada umarnin a kama shi duk inda aka gan shi

Kwamitin da aka ƙaddamar ya fara bin hanyoyin aiwatar da sabbin tsare tsare wanda shugaban ƙasa ya furtasu kwana kwanan nan, wanda suke da nufin jawo masu ƙoƙari da ƙwaƙwalwa zuwa cikin harkar koyarwa.

A cewar FG, hakan zai bawa malamai ƙarfin guiwa wajen gudanar da ayyukansu da kuma fitar da gogaggun ɗalibai masu hazaƙa don bunƙasa cigaban ƙasa.

Karin albashin Malamai: Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da kwamitin aiwatarwa
Ministan ilimi; Adamu Adamu
Asali: Facebook

Wasu daga cikin tsare-tsaren sun haɗar da; Albashi na musamman ga malamai masu koyar da masu buƙata ta musamman.

Ƙara wa'adin barin aiki da shekarun koyarwa, Fansho na musamman ga malamai masu koyar da masu buƙata ta musamman, ƙarawa aikin koyarwa matsayi da cancanta ga malaman gwamnati da kuma bada alawus na musamman ga malamai.

KARANTA: Batan tiriliyan uku da biliyan fiye da ashirin: Majalisa ta gayyaci Malam Kyari da Emefiele

Da yake ƙaddamar da kwamitin, Ministam Ilmi, Mallam Adamu Adamu, ya bada tabbacin bada dukkan wata gudunmawa da ake buƙata ɗon aiwatar da tsare-tsaren cikin tsanaki da nutsuwa.

A maganganun da yayi ya ce; "Shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya yarda cewa harkar koyarwa ita ce babbar hanyar da zata habbaƙa ta kuma bunƙasa cigaba a ƙasa.

"Saboda haka, ilmi, sadaukarwa, da kuma iyawa sune nagarta da za'a ke dubawa kafin ɗaukar yayayyun ɗalibai daga manyan makarantunmu zuwa ajuzuwa, sai kuma gudunmawar da suke bayarwa wajen cigaban ƙasa."

Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya ce jami'o'i masu zaman kansu da kasashen ketare sai tsince mambobinsu suke yi a yayin da gwamnati ta barsu suna yajin aiki har yanzu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng