'Yan bindiga sun kashe tsohon shugaban NUPENG bayan garkuwa da shi a Rivers

'Yan bindiga sun kashe tsohon shugaban NUPENG bayan garkuwa da shi a Rivers

- Yan bindiga sun bi tsohon shugaban kungiyar NUPENG na jihar Rivers har gidansa sun sace shi

- An tsinci gawarsa a Peter Odili Road kwana guda bayan da masu garkuwar suka sace shi tare da alamun harbin bindiga a jikinsa

- Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da mutuwarsa kuma ta fara bincike don gano wadanda suka aikata laifin

'Yan sanda a Jihar Rivers sun tabbatar da sace tare da kashe tsohon shugaban kungiyar kwadago ta ma'aikatan dakon man fetur NUPENG, Ebenezer Kalabo Amah kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka bi Amah har gidansa da ke Precious Chukwu Street a karamar hukumar Obio/Akpor suke yi awon gaba da shi yayin da ya ke kokarin shiga gida a ranar Laraba 18 ga watan Nuwamba.

'Yan bindiga sun kashe tsohon shugaban NUPENG bayan garkuwa da shi
'Yan bindiga sun kashe tsohon shugaban NUPENG bayan garkuwa da shi. Hoto daga @MobilePunch
Asali: UGC

Kakakin 'yan sandan jihar, Nnamdi Omoni yayin tabbatar da afkuwar lamarin ya ce an gano motar marigayin a ranar da aka sace shi sannan aka tsinci gawarsa a Peter Odili Road a ranar Alhamis.

DUBA WANNAN: 'Na gwammace a datse min kai a maimakon in bada haƙuri', martanin Bashir El Rufai ga masu sukar hotunansa da Nwakaego

Omoni ya ce, "Eh, zan iya tabbatarwa. An sace shi a Woji a ranar 17 ga watan Nuwamba. A ranar 'yan sanda sun gano motarsa. Yayin da muke cigaba da nemansa, mun samu labarin cewa an yarda gawarsa a wani wuri a Peter Odili Road.

"Don haka mun tafi wurin a ranar 18 ga watan Nuwamba sannan muka tabbatar shine dai mutumi da aka yi garkuwa da shi tunda farko. An dauke gawarsa an kai asibiti.

"Motarsa na hannun mu. An fara bincike don gano yadda abin ya faru don kama wadanda ake zargin su suka aikata wannan mummunan lamarin."

KU KARANTA: A dena kira na 'Special One', Mourinho ya bayyana sabon sunan da ya ke so

Mataimakin Shugaban Kungiyar Masu Sana'o'i na Kasa, Chika Onuegbu yayin tsokaci kan batun ya ce, "ETK Amah mutumin kirki ne da ke wanzar da farin cikin duk inda ta tafi. Abin bakin ciki ne. Allah ya jikansa."

Mafi yawancin tsaffin abokan aikin mu a SPDC da Kungiyar Kwadago su kan kira shi ETK.

A wani labarin, an kama wata mata mai shekaru 40 da haihuwa mai suna Ruqayya Rabi'u a Jigawa bayan samun ta da jabun kuɗade (dubu ɗai-dai guda 100 da ɗari biyar-biyar guda 76) a ƙaramar hukumar Birnin Kudu.

Wacce ake zargin dai ƴar asalin ƙaramar hukumar Bichi ne a Kano ta shiga hannu ne bayan ta siya man shafawa na N300 a kasuwa kamar yadda LIB ya ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel