Babu shirin sake sauya-sheka zuwa Jam’iyyar APC inji Gwamna Ortom

Babu shirin sake sauya-sheka zuwa Jam’iyyar APC inji Gwamna Ortom

- Gwamna Samuel Ortom ya yi martani a kan rade-radin zai koma APC

- Hadimin Gwamnan ya ce babu abin da zai sa maigidan na sa ya bar PDP

- Ortom ya ce wasu sun nemi ya koma APC, amma ya ce ba za ayi haka ba

Gwamna Samuel Ortom ya ce bai da niyyar koma wa jam’iyyar APC mai mulki wanda ya bar ta tun tuni, ya shiga jirgin PDP, har ya lashe zaben 2019.

Vanguard ta ce gwamnan ya fita da jawabi ne ta babban sakatarensa na yada labarai, Terver Akase a garin Makurdi, a ranar 19 ga watan Nuwamba, 2020.

Jawabin da hadimin gwamnan ya fitar ya shiga hannun hukumar dillancin labarai na kasa, NAN.

KU KARANTA: Wasu Gwamnonin PDP za su dawo cikinmu - Gwamnan Kogi

Kamar yadda jawabin ya nuna, wasu fitattun mutane sun tuntubi gwamnan domin ya yi watsi da jam’iyyarsa ta PDP, amma ya ki karbar goron gayyatarsu.

Jawabin ya ke cewa: “Mun karanta wasu bayanan banza cewa ‘ya ‘yan APC a jihar Benuwai sun nuna gwamna Samuel Ortom ya na shirin sake shiga APC.”

Terver Akase a madadin gwamnan, ya ce: “Masu hannu a wannan rade-radi su na nema ne su more bakunansu.”

“A kan me gwamna Ortom zai koma jam’iyyar APC? Ya yi mene?”

KU KARANTA: Abin da zai faru da Umahi bayan ya koma APC - PDP

Babu shirin sake sauya-sheka zuwa Jam’iyyar APC inji Gwamna Ortom
Ortom ya ce ya na nan a PDP daram-dam-dam Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC

Sakataren gwamnan ya ce a matsayin Ortom na jagoran PDP a Benuwai da kuma yankinsa na Arewa ta tsakiya, lafiya lau ya ke zaune da duk ‘yan jam’iyya.

“Saboda haka abin dariya ne wani ya fara kyankyasa cewa gwamnan ya na neman barin PDP.” Akase ya ba su fadi wannan labari, su guji yada karyayyaki.

A gefe guda kuma kun ji cewa jam’iyyar APC ta gamu da gagarumin rashi yayin da PDP ta karbe mata magoya-baya fiye da 4,000 a garin Ogbomoso, jihar Oyo.

Jam’iyyar PDP ta na kara sirka karfin APC domin ganin ta sake samun nasara a zaben 2023

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel