Hukuncin Ubangiji na bi, na sauya sheka zuwa jam'iyyar APC, Umahi

Hukuncin Ubangiji na bi, na sauya sheka zuwa jam'iyyar APC, Umahi

- A ranar Talata, Umahi ya bayyana dalilansa na sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC

- Ya ce komawarsa jam'iyyar APC yardar Ubangiji ne, da kuma girmama shugaba Buhari

- Ya ce shugaba Muhammadu Buhari adali ne, ba ya nuna bambanci tsakanin gwamnoninsa

A ranar Talata, Umahi ya sanar da sauya sheka zuwa jam'iyyar APC, bayan 'yan satittuka da aka yi ta rade-radin fitarsa daga jam'iyyar PDP, jaridar The Cable ta wallafa.

Yayin da yake jawabi a wani taro na kungiyar gwamnonin arewa a ranar Alhamis, Umahi ya ce ya koma jam'iyyar APC ne saboda bin zabin Allah da kuma shugaba Muhammadu Buhari.

A cewarsa, "Komawa ta APC, yarda ce ga zabin Ubangiji da kuma nuna kauna ga shugaba Muhammadu Buhari, da kuma mutane ma'abota daraja da ke jihar Ebonyi.

"A wurin mutane, kudi shine komai, amma a wurina na zabi basira daga Ubangiji. Mutane suna ta tambayata dalilin da yasa na bar PDP, idan jam'iyyar APC za ta yi min adalci a lokacin da bana cikinta, ina ga ina cikinta?

"Ina ce musu, duk girman PDP, mutum daya ne yake fadi a ji, amma APC kuma tana bai wa kowa dama."

Umahi ya ce Buhari yana iyakar kokarin yi wa kowa adalci, ko da kuwa ba dan jam'iyyarsa bane.

Ya tunatar da lokacin da Buhari ya amince da biyan Naira biliyan 10, don gyaran tashar jirgin Akanu Ibiam da ke jihar Enugu, ba tare da wani sharadi ba.

Ya ce a matsayinsa na shugaban gwamnonin kudu maso gabas, ya bukaci kudaden kuma a lokacin yana jam'iyyar PDP. Ya bayyana adalcin Buhari a matsayinsa na shugaba, yadda ba ya nuna rashin adalci a tsakanin gwamnoninsa.

KU KARANTA: Tsoho mai shekaru 69 ya ce bai taba zuwa asibiti ba don bai taba ciwo ba

Hukuncin Ubangiji na bi, na sauya sheka zuwa jam'iyyar APC, Umahi
Hukuncin Ubangiji na bi, na sauya sheka zuwa jam'iyyar APC, Umahi. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Innalillahi: Tsohon malami a KADPOLY ya harba matarsa tare da kashe kansa

A wani labari na daban, Gwamnonin jihohin arewa sun ce a shirye suke da su saurari matasan yankin a kan matsalolin da suke fuskanta.

Shugaban kungiyar gwamnonin arewa, Simon Lalong, ya fadi hakan a ranar Laraba a Kaduna yayin taron rantsarwar kwamitin matasa, wacce aka kirkira musamman don samar da mafita ga yankin.

A wata takarda da jami'in hulda da jama'ar gwamnan, Macham Makut ya saki, ya ce wajibi ne samar da ayyukan yi, kawar da jahilci, ta'addanci da talauci ga matasa ta hanyar kirkirar kwamiti.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel