FG za ta yi ƙarar ASUU a kotu

FG za ta yi ƙarar ASUU a kotu

- Gwamnatin tarayya ta ce idan har bata da wani zabi za ta iya maka kungiyar malaman jami'a ASUU a kotu kan yajin aiki

- Ministan Kwadago da Ayyuka, Chirs Ngige ne ya yi wannan barazanar a karshen taron da suka gudanar da malaman a ranar Laraba yayin zantawa da manema labarai

- An dai dade ana ta yin tarurruka tsakanin gwamnatin da kungiyar malaman kan yajin aikin da suke yi na tsawon watanni bakwai amma har yanzu ba a cimma matsaya ba

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi barazanar shigar da kungiyar malaman jami'ar Najeriya, ASUU, kara a kotun ma'aikata kan yajin aikin da ta ke yi da ya-ƙi-ci-yaƙi-cinyewa kamar yadda TVC ta ruwaito.

Ministan Kwadago da Ayyuka, Dakta Chris Ngige ne ya yi wannan barazanar a karshen taron da suka yi na tsawon kimanin awa uku da shugbannin kungiyar a Abuja.

FG za ta yi ƙarar ASUU a kotu
FG za ta yi ƙarar ASUU a kotu. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Wani mutum ya yi barazanar kai coci kotu idan bata biya shi kuɗin baikonsa na shekaru 19 ba

Kamar yadda suka saba, bangarorin biyu sun bayyana fatar ganin an kawo karshen yajin aikin a jawabinsu na bude taron.

Amma bayan kimanin awa biyu cikin taron, ASUU ta ce har yanzu babu wani sabon abu da aka gabatar mata.

KU KARANTA: Mutum 10 sun mutu sakamakon trela da ta afka musu a kasuwa

A hirar da ya yi da manema labarai, Ministan ya ce akwai yiwuwar gwamnati ta dauki matakin shari'a kan malaman jami'ar da ke yajin aiki don kawo karshen rashin jituwar.

A wani labarin daban, kungiyar ta ASUU ta ce kada iyaye su yi tunanin cewa abin da suke nema ya yi yawa da har zai sa su dauki dogon lokaci suna yajin aiki.

Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar ta bayyana cewa iyaye su lura cewa idan gwagwarmayarsu ta tashi a banza, "aljihun su zai koka wajen tura yaran su karatu jami'a."

Shugaban ASUU shiyyar Lagos, Prof. Olusiji Sowande ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai jim kadan bayan taron tattaunawa da kungiyar tayi a jami'ar Olabisi Onabanjo University (OOU), Ago-Iwoye, a jihar Ogun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel