Batan tiriliyan uku da biliyan fiye da ashirin: Majalisa ta gayyaci Malam Kyari da Emefiele

Batan tiriliyan uku da biliyan fiye da ashirin: Majalisa ta gayyaci Malam Kyari da Emefiele

- Batun batan makudan kudade daga asusun gwamnati Najeriya da karkatar da kudaden haraji ba bakon abu bane

- A wannan karon, majalisar wakilai ta ce tiriliyan uku da biliyan ashirin da hudun sun yi batan dabo, ba a san yadda aka yi da su ba

- Majalisar ta ce ya zama wajibi gwamnan CBN da shugaban NNPC su bayyana a gabanta domin yin bayani a kan makomar kudade

Majalisar wakilan Najeriya ta aika takardar gayyata zuwa ga shugaban kamfanin mai na kasa (NNPC) da kuma gwamnan babban bankin kasa (CBN) domin su yi bayani a kan batan dabon wasu kudade masu nauyin gaske.

A cewar majalisar, Naira tiriliyan uku da biliyan ashirin da hudu sun bata daga cikin kudaden cinikayyar man fetur a shekarar 2014.

Dan majalisa, Wole Oke, mai shugabantar kwamitin kula da asusun gwamnatin tarayya ya ce bayanai daga ofishin babban mai binciken kudi na tarraya ne suka nuna hakan.

DUBA WANNAN: Sojoji sun ragargaji 'yan bindiga a Katsina, sun kashe na kashewa, sun kwaci makamai da dukiya

Honarabul Oke ya ce bayan kwamitinsa ya samu bayanai da shaidun batan kudin, ya aika takardar tuhuma zuwa NNPC da CBN.

Batan tiriliyan uku da biliyan fiye da ashirin: Majalisa ta gayyaci Malam Kyari da Emefiele
Shugaba Buhari yayin gabatar da kasafin kudin shekarar 2021 a majalisa @NGRpresident
Asali: Twitter

Kwamitin ya ce akwai bukatar shugaban NNPC, Malam Mele Kyari, da gwamnan CBN, Godwin Emefiele, su bayar da bayani a kan batan kudaden.

Duk da kwamitin ya koka a kan cewa Kyari ya ki amsa gayyatar da aka taba yi masa a baya, ya ce ya zama farilla yanzu ya amsa gayyata domin sanar da yadda aka yi da kudaden.

DUBA WANNAN: Kwamandan soji ya yanke jiki ya fadi matacce yayin bayar da horo a kan yaki da Boko Haram

Legit.ng Hausa ta taba rawaito Kyari ya na cewa makusanta shugaban kasa ne su ka ci moriyar tallafin man fetur sabanin talakawan Najeriya da ake fitar da kudin tallafin dominsu.

A wata hira da aka yi da shi a wani gidan Radiyo da ke Kaduna, Kyari ya bayyana cewa an janye tallafin ne saboda kwalliya ta gaza biyan kudin sabulu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel