Kotu ta bada umurnin kama ɗan Atiku Abubakar kan batun rikon ƴaƴa

Kotu ta bada umurnin kama ɗan Atiku Abubakar kan batun rikon ƴaƴa

- Wata babbar kotu a Abuja ta bada umarnin kama dan gidan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar bisa bijerewa umarnin ta

- Kotun dai ta bada umarnin da ya mika yayan sa uku a hannun mahaifiyarsu Maryam Sherif wanda ta shigar da kara ta nemi da ya bata yayan bayan ya sake ta

- Lauyan mai kara ne ya bukaci kotu da ta bada umarnin kama Abubakar bayan da ya gaza halartar zaman kotun ranar Alhamis duk kuwa da samun takardar sammaci

Wata babbar kotu, a Kubwa, Abuja, a ranar Alhamis, tayi umarnin gaggauta kama dan gidan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, bisa bijerewa wani umarni da kotu tayi ranar 27 ga Oktoban 2020 wanda ke umartar sa da mika yayansa uku ga mahaifiyarsu, Maryam Sherif, saboda tsaro.

Matar dai ita ce ta shigar da karar kan ya bata yayan bayan mijin nata, Abubakar, wanda ya ke amsa sunan kakansa lamar yadda The Punch ta ruwaito.

Alkalin, Bashir Danmaisule ya yanke hukunci ranar 27 ga Oktoba 2020, inda ya yi umarni a mikawa Maryam yaran.

Amma lauyan ta, Nasir Saidu, ya sake shigar da korafi akan cewa Abubakar ya gaza cika umarnin.

Saidu ya roki kotu da ta nemi wanda ake karar da ya bayyana a gaban kotu ya yi bayanin dalilin da yasa bai cika umarnin kotun.

Kotu ta bada umurnin kama dan Atiku Abubakar
Kotu ta bada umurnin kama dan Atiku Abubakar. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Na gwammace a datse min kai a maimakon in bada haƙuri', martanin Bashir El Rufai ga masu sukar hotunansa da Nwakaego

Da Abubakar da lauyansa Abdullahi Hassan, basu halarci zaman kotun ranar Alhamis ba, duk da cewa ya samu takardar sammaci ta hannun hukumar hana fasakwabri (kwastam) inda ya aiki, tun ranar 3 ga Nuwamba 2020.

Da yake dogaro da wannan batu, Saidu ya roki kotun da ta bada umarnin kama wanda ake karar.

KU KARANTA: Yan jam'iyyar APP 20,000 ciki da shugbansu sun koma PDP a Ebonyi

Ya tunawa kotun cewa wanda ake karar ya sha bijerewa umarnin kotun na kin zuwa da yaran a kowane zaman kotu lokacin sauraren karar.

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Danmaisule ya ce Abubakar bai halarci shari'ar ba duk da samun takardar sammaci.

Da yake yanke hukunci da sashe na 26 na kotunan birnin tarayya Abuja, ya bada umarnin "gaggauta kama wanda ake karar."

A wani labarin, an kama wata mata mai shekaru 40 da haihuwa mai suna Ruqayya Rabi'u a Jigawa bayan samun ta da jabun kuɗade (dubu ɗai-dai guda 100 da ɗari biyar-biyar guda 76) a ƙaramar hukumar Birnin Kudu.

Wacce ake zargin dai ƴar asalin ƙaramar hukumar Bichi ne a Kano ta shiga hannu ne bayan ta siya man shafawa na N300 a kasuwa kamar yadda LIB ya ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel