Kotu ta sake daga cigaba da sauraron shari'ar Zakzaky zuwa 2021 bayan sauraron shaidu hudu

Kotu ta sake daga cigaba da sauraron shari'ar Zakzaky zuwa 2021 bayan sauraron shaidu hudu

- A ranar Laraba ne babbar kotun jihar Kaduna ta sake zama domin sauraron shari'ar Shugaban ƙungiyar Shi'a, Sheik Ibrahim El-Zakzaky, da matarsa, Zeenat

- Bayan sauraron shaida daga wasu manyan sojoji guda biyu; Janaral da Kanal, kotun ta gada cibaga da suraron shari'ar zuwa ranar Alhamis

- Alkalin kotun, Jastis Gideon Kurada, ya sake daga cigaba da sauraron karar zuwa watan Janairu na shekarar 2021

A ranar Alhamis ne wata babbar kotun jihar Kaduna ta sake daga sauraron shari'ar shugaban kungiyar Shi'a, Sheikh Ibrahim El-zakzaky, zuwa ranar 25 ga watan Janairu na shekarar 2021.

Alkalin kotun, Jastis Gideon Kurada, ya daga Shari'ar ne bayan shaidu hudu sun bayar da shaida a zaman kotun na ranar Alhamis.

Gwamnatin jihar Kaduna ta gurfanar da El-zakzaky da matarsa, Zeenat, bisa tuhuma guda takwas da suka hada da zargin haddasa rashin rayuka da taro ba bisa ka'ida ba da hana jama'a zaman lafiya da sauransu.

A ranar 29 ga watan Satumba ne El-zakzaky da matarsa suka ce basu aikata laifukan da ake zarginsu dasu ba.

KARANTA: Kotu ta janye belin Abdulrasheed Maina, ta bada umarnin a kama shi duk inda aka gans hi

Wani Manjo Janaral da Kanal ɗin soji sun bada shaidarsu a gaban alƙali Kurada akan shari'ar El-Zakzaky da matarsa Zeenat a ranar Laraba.

Kotu ta sake daga cigaba da sauraron shari'ar Zakzaky zuwa 2021 bayan sauraron shaidu hudu
Zakzaky da Zeenat
Asali: UGC

Jagoran lauyoyi masu kare Zakzaky, Femi Falana, a lokacin da yake magana da manema labarai bayan zaman kotun, ya ce an ɗage shari'ar zuwa 19 ga Nuwamba, 2020 don cigaba da sauraron ƙarar.

Da ya ke magana da manema labarai ranar Alhamis bayan zaman kotun, Falana ya ce daga cikin wadanda suka bayar da shaida a ranar Alhamis akwai wani tsohon darekta a hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).

KARANTA: Arzikin gwal din Zamfara ba na gwamnati bane, in ji kwamishina Nurudden Isa

"Masu kara sun kira shaidu guda hudu a yau, tsohon darekta a DSS da sauran wasu mutane uku da suka yi ikirarin cewa su makwabtan El-Zakzaky ne.

"Sun bayar da shaida. Sun yi magana ne musamman a kan alakarsu da wanda muke karewa.

"Shi jami'in DSS din ya ce sun kula da wanda mu ke karewa a lokacin da sojoji suka mayar da shi hannunsu domin su ajiye shi.

"Mun yi musu tambayoyi kuma sun bamu amsa kafin daga bisani a daga cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 25 ga watan Janairu na shekarar 2021," a cewar Falana.

NAN ta rawaito cewa ya zuwa yanzu mutane shidda sun bayar da shaida a gaban kotun tun bayan fara sauraron shari'ar.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, ƴan sanda a jihar Kano sun ƙwamushe wani saurayi mai shekaru 24 bisa zargin aikita laifin kisa da garkuwa da wata yariya ƴar shekara takwas, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN).

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng