Arzikin gwal din Zamfara ba na gwamnati bane, in ji kwamishina Nurudden Isa

Arzikin gwal din Zamfara ba na gwamnati bane, in ji kwamishina Nurudden Isa

- An samu barkewar cece-kuce bayan gwamnatin Zamfara ta sanar da cewa za ta fara cinikayyar gwal din da aka gano a jihar

- Gwamnonin kudancin Najeriya sun nemi ba'asi a kan dalilin da zai sa Zamfara ta siyar da gwal dinta amma Delta ba zata sayar da man fetur din jihar ba

- Dakta Nurudden Isa, Kwamishina mai kula da albarkatun kasa a Zamfara, ya ce arzikin gwal din ba na gwamnati bane

Kwamishina mai kula da albarkatun kasa a jihar Zamfara, Dakta Nurudden Isa, ya ce arzikin gwal din Zamfara ba mallakar gwamnati bane.

Dakta Isa ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a ofishinsa ranar Laraba a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

A cewarsa; "gwamnatin jiha ba ta mallaki ko takun kafa na fili a wurin da ake hakar gwal ba."

Kwamishinan ya kafe a kan cewa gwamnati na sayen gwal din ne daga hannun masu hakarsa domin hana ficewa da shi daga cikin Najeriya ko Kuma a siyarwa 'yan bindiga dadi.

KARANTA: Cacar bakin manya: IGP Adamu ya mayar wa da Janar Garba martani

"Ita gwamnatin jiha ta na siya ne kawai domin tabbatar da cewa bai shiga hannun batagari da zasu siyar da shi domin siyen makamai ba.

Arzikin gwal din Zamfara ba na gwamnati bane, in ji kwamishina Nurudden Isa
Gwamna Matawalle da gwal @Premiumtimes
Asali: Twitter

Kazalika, kwamishinan ya kara da cewa gwamnati jihar Zamfara ta haramta hakar gwal tare da fadin cewa "duk mai son shiga kasuwancin hakar gwal sai ya samu izini daga gwamnatin tarayya."

Kwamishinan ya kara da cewa albarkatun karkashin kasa mallakar gwamnatin tarayya ne kuma ita kadai keda ikon bayar da lasisi.

KARANTA: Ba zaku iya kamani ba; Shekau ya zolayi sojoji a sabon bidiyo

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa wanda ya shafi jihar Zamfara; a kalla tsofin kansiloli 69 ne daga kananan hukumomi 14 suka sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP, kamar yadda Punch ta rawaito.

Hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa da Jamilu Iliyasu, sakataren yada labaran gwamna Bello Matawalle, ya fitar a ranar Talata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng