Ana wata ga wata: Ana zargin Kwamandan Hisbah da lakume kayan tallafin korona a Kano
- Jami'an hukumar Hisbah na karamar hukumar Dala a jihar Kano, suna zargin kwamadansu da yin sama da fadi a kan kason da aka basu na tallafin korona
- Kayayyakin da ake zarginsa da lakumewa sun hada da buhuhunan shinkafa 50, kwalayen taliya 50 da kuma kwalayen Indomie 50
- Sai dai hekwatar hukumar ta jihar ta bayyana cewa tuni ta fara gudanar da bincike a kan lamarin
Rahotanni sun kawo cewa jami’an hukumar Hisbah ta karamar hukumar Dala a jihar Kano, suna zargin kwamandan hukumar a yankin, Malam Suyudi Muhammad Hassan, da yin sama da fadi a kan nasu kason na kayan tallafin korona.
An dai tattaro cewa karamar hukumar Dala ta ba ma'aikatan hukumar kaso na tallafin korona don rage radadin kullen da aka yi saboda annobar.
A cikin wata takardar shigar da korafin wanda jami’an hukumar kimanin su 73 suka tura wa hedkwatar hukumar ta jiha, sun nemi babban kwamandan hukumar, Ustaz Harun Ibn Sina ya gudanar da bincike a kan al’amarin.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai hari gidan wani tsohon gwamna, sun kashe dan sanda
A cewar takardar korafin, kayayyakin da ake zargin kwamandan da yin sama da fadi a kai sun hada da "buhuhunan shinkafa 50, kwalayen taliya 50 da kuma taliyar Indomie kwalaye 50."
Har ila yau jami’an, sun bayyana cewa tun daga lokacin da karamar hukumar ta bayar da kayayyakin aka neme su aka rasa, inda ake zargin ya karkatar da su, Aminiya ta ruwaito.
A halin yanzu ba a ji ta bakin kwamandan da ake zargi ba, kamar yadda rahoton ya bayyana, baya amsa kiran wayar da aka yi masa sannan bai amsa sakon waya ba.
Har wa yau rahoton ya bayyana cewa da aka tuntubi hedkwatar hukumar, jami’in hulda da jama’a na hukumar, Malam Lawan Fagge ya ce ba zai iya cewa komai ba kasancewar hukumar na gudanar da bincike akan lamarin yanzu haka.
KU KARANTA KUMA: Buhari ya mika sakon gaisuwa ga tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan yayinda ya cika shekaru 63
A karshe ya bayyana cewa tuni hukumar ta gayyaci kwamadan domin ya amsa tambayoyi sannan kuma cewa a yanzu haka suna ci gaba da gudanar da bincike.
A wani labari na daban, Hukumar Hisbah reshen Jihar Katsina da lalata giya fiye da 300 uku da ta kama cikin kwallabe da gwamgwanaye a sassan Jihar.
Ma'aikatan hukumar Hisban na karamar hukumar Daura ne suka gudanar da wannan aikin a ranar Talata 17 ga watan Nuwamban 2020. R
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng