'Yan bindiga sun sace ƴan gida ɗaya su biyar a Abuja
- Ana cigaba da samun ƙaruwar matsalar garkuwa da mutane a yankin Arewacin Najeriya
- Wasu ƴan bindiga sun yi awon gaba da ƴan gida ɗaya su biyar a Pegi da ke babban birnin tarayya Abuja
- Ƴan bindigan sun bi su har gidansu misalin ƙarfe 11 na daren Litinin 16 ga watan Nuwamba suka tisa ƙeyarsu
Wani rahoton da Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa an sace wasu ƴan gida ɗaya su biyar a garin Pegi da ke ƙaramar hukumar Kuje a Abuja.
A cewar rahoton, wadanda aka yi garkuwa da su sun hada da Jubril Abdullateef (22), Sherifat Abdullateef (20), Muyidat Abdullateef (13) Nura Abdullahi (18) da Nahimat Abdullahi (9).
Ƴan bindigan sun afka gidansu misalin ƙarfe 11 na daren ranar Litinin 16 ga watan Nuwamba inda suka sace su a cewar rahoton.

Asali: UGC
KU KARANTA: Wike ya ce wani gwamnan PDP daya zai sake fita daga jam'iyyar
Wani maƙwabcinsu ya ce;
"Mahaifinsu baya gida don ya tafi gidan ɗayan matarsa ya kwana a lokacin da ƴan bindigan suka afka gidan.
"Ƴan bindigan sun kwace wayar mahaifiyarsu suka umurce ta da yaranta su fita waje a lokacin da tayi yunkurin kirar mai gidan."
DUBA WANNAN: Katin gayyatar ɗaurin auren Bashir El-Rufai da Nwakaego ya fito
Ya ce ƴan bindigan sun kwace kimanin minti 20 ba tare da yin karbi ba sannan suka tsere da yaran kafin ƴan sanda da sojojin ruwa da ke kusa da unguwar su iso.
Kakakin kungiyar cigaban Pegi, Oyedeji Oyetunji ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce;
"Abinda muke fuskanta a Pegi shine wasu ƴan bindiga sun shiga gidan maƙwabtan mu sun sace ƴan gida ɗaya su biyar."
Da aka tuntube shi, Kakakin ƴan sandan Abuja, ASP Mariam Yusuf ta ce, "Ka ɗan dakata, za mu fitar da sanarwa game da afkuwar lamarin."
A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, gwamnatin Jihar Kogi za ta bullo da sabon haraji a kan kowanne gasashen burodi a jihar kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Ma'aikatar kasuwanci da masana'antun tace harajin zai taimaka wajen kara samun kudaden shigar da ake samu na cikin gida.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng