An yankewa saurayi hukuncin kisa ta hanyar rataya dalilin kashe masoyiyarsa

An yankewa saurayi hukuncin kisa ta hanyar rataya dalilin kashe masoyiyarsa

- Wani saurayi mai shekaru 39, Musiliu Owalabi, ya kashe masoyiyarsa, Miss Afusat Idowu, a jihar Ogun

- Owalabi ya amsa laifinsa tare da jagorantar tawagar jami'an 'yan sanda zuwa wurin da ya binne Afusat bayan ya kashe ta

- Duk da mai laifin ya ki yarda da tuhumar da ake yi masa, mai shari'a Mosunmola Dipeola, ta yanke masa hukuncin kisa

Wata babbar kotu a Abeokuta, jihar Ogun, a ranar Laraba, ta yankewa wani bakanike mai shekaru 39, Musiliu Owalabi, hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kashe masoyiyarsa, Miss Afusat Idowu.

Alƙaliyar alƙalan jihar Ogun, Mai shari'a Mosunmola Dipeola, ta yankewa Owolabi hukunci bayan samunsa da laifin kisan kai.

Ta yanke hukuncin ne bayan an tabbatar da zargin da ake yiwa Owolabi a matsayin mai laifin.

Dipeola tayi amfani da dokar hana kisa ta sashe na 319 da kundin miyagun laifuka na jihar Ogun da aka yi wa gyara a shekarar 2006.

Da farko, masu tuhuma sun ce wanda ake zargin ya aikata laifin ne ranar 1 ga watan Fabarairu, 2018, a yankin 'Camp area' a Abeokuta.

KARANTA: Arzikin gwal din Zamfara ba na gwamnati bane, in ji kwamishina Nurudden Isa

Mai gabatar da kara, Mista James Mafe, ya ce wanda ake zargin ya ɗauki Afusat zuwa Otel don sharholiyarsu,inda bayanan ta fara ƙorafin cikinta yana ciwo.

"Sai ya ɗauketa zuwa motarsa. A hanyarsa ta dawo ne ya fahimci cewa budurwa ta mutu, daga nan sai ya ɗauketa a sirrance ya kai gawar wani kango, ya haƙa dan ƙaramin rami ya binneta ba tare da ya shaidawa kowa ɓa.

An yankewa saurayi hukuncin kisa ta hanyar rataya dalilin kashe masoyiyarsa
An yankewa saurayi hukuncin kisa ta hanyar rataya dalilin kashe masoyiyarsa
Asali: UGC

"Asirin wanda ake zargin ya tonu bayan ƙanin buduruwar tasa ya shigar da ƙorafi a ofishin ƴansanda, inda ya bayyana musu cewa tun bayan fitar yayarsa zuwa bikin suna a unguwar Bode Olude ba'a sake jin ɗuriyarta ɓa," kamar yadda masu tuhumar suka bayyana.

Ya kara da cewa; "lokacin da ake tsaka da bincike, ƴansanda sun gano shine mutum na ƙarshe da suka gana da buduruwar.

KARANTA: Shari'ar Sheik Zakzaky: Manjo Janaral da Kanal sun bada shaida a kotu

"Ba tare da wata wata ba, muka daƙume shi inda ba tare da wata gardama ba ya amsa laifinsa har ya kai ƴansanda inda ya binne masoyiyar tasa" Mafe ya yi ƙarin haske.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya rawaito cewar an gurfanar da wanda ake zargin tun 12 ga watan Nuwamba 2019.

Sai dai yayi roƙon shi ba mai laifi bane.

A jihar Kano kuwa wani saurayi ne mai shekaru 24 ya shiga hannu bisa zargin aikita laifin kisa da garkuwa da wata yariya ƴar shekara takwas, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN), kamar yadda Legit.ng ta rawaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel