Shari'ar Sheik Zakzaky:Manjo Janaral da Kanal sun bada shaida a kotu,za'a cigaba da sauraron ƙara ranar Alhamis.

Shari'ar Sheik Zakzaky:Manjo Janaral da Kanal sun bada shaida a kotu,za'a cigaba da sauraron ƙara ranar Alhamis.

- A ranar Laraba ne babbar kotun jihar Kaduna ta sake zama domin sauraron shari'ar Shugaban ƙungiyar Shi'a, Sheik Ibrahim El-Zakzaky, da matarsa, Zeenat

- Yayin zaman kotun, wani Manjo Janaral da Kanal ɗin soji sun bada shaidarsu a gaban alƙali Gideon Kurada

- Gwamnatin jihar Kaduna ta na tuhumar Zakzaky da matarsa da aikata laifin kisan gilla da kuma shirya taro ba bisa ka'ida ba

Wani Manjo Janaral da Kanal ɗin soji sun bada shaidarsu a gaban alƙali Gideon Kurada na babbar kotun jihar Kaduna akan shari'ar Shugaban ƙungiyar Shi'a ta Najeriya(IMN),Sheik Ibrahim El-Zakzaky da matarsa Zeenat.

Jagoran lauyoyi masu kare Zakzaky, Femi Falana, a lokacin da yake magana da manema labarai bayan zaman kotun, ya ce an ɗage shari'ar zuwa 19 ga Nuwamba, 2020 don cigaba da sauraron ƙarar.

KARANTA: Arzikin gwal din Zamfara ba na gwamnati bane, in ji kwamishina Nurudden Isa

"Zakzaky bai mutu ba, magoya bayan Zakzaky suna buƙatar a sakar musu mutanensu", a cewarsa.

"An karɓi shaidu biyu, Manjo Janaral da kuma Kanal. Suna daga cikin shaidu 18 da aka tsara za'a karɓi shaidunsu don gasgata laifin waɗanda yake karewa.

Shari'ar Sheik Zakzaky:Manjo Janaral da Kanal sun bada shaida a kotu,za'a cigaba da sauraron ƙara ranar Alhamis.
Sheik Zakzaky da matarsa, Zeenat
Asali: Facebook

"An yiwa jami'an tambayoyin tsanaki, kuma sun bada shaidar atisayen da ya wakana tsakanin 12 zuwa 14 ga watan Disambar shekarar 2015, da kuma irin rawar da sojoji suka taka a atisayen," a cewar Falana.

Ya kuma roƙi hukumomi da su daina rufe tituna duk lokacin da za'a saurari shari'ar, "an fara sauraron ƙara ba tare da kawo wanda nake karewa ba. A saboda haka ina roƙom hukumomi da su daina rufe tituna don bawa jama'a haƙƙinsu na cigaba da gudanar da harkokinsu, musamman mazauna wurin".

KARANTA: Cacar bakin manya: IGP Adamu ya mayar wa da Janar Garba martani

Dari Bayero, wanda ya jagoranci tuhumar, ya bar harabar kotun ba tare da magana da ƴan jarida ba.

Jaridar Daily Trust ta kalato cewa shugaban ƙungiyar Shi'a (IMN), a ranar 29 ga watan Satumba, 2020, ya yi roƙon cewa bashi da laifi ko hannu akan tuhumarsa da ake da har laifuka takwas bisa zargin kisan kai da ake tuhumarsa da aikatawa.

Ana cigaba da sauraron ƙarar shugaban ƙungiyar Shi'a (IMN)Zakzaky da matarsa Zeenat bisa zargin kisan gilla, haɗa haramtaccen taro da kuma hana al-umma zaman lafiya da sauran zarge zarge.

Sauraron shari'ar Sheikh El-Zakzaky da matarsa, Zinat, ya cigaba a babbar kotun shari'a ta birnin Kaduna, kamar yadda Legit.ng Hausa ta rawaito tun da safiyar ranar Laraba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel