Ba zaku iya kamani ba; Shekau ya zolayi sojoji a sabon bidiyo

Ba zaku iya kamani ba; Shekau ya zolayi sojoji a sabon bidiyo

- Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya fitar da sabon bidiyo mai tsawon minti talatin

- A cikin sabon faifan bidiyon, Shekau ya zolayi rundunar soji tare da sanar da cewar ba zasu iya kama shi ba saboda aikin Allah ya ke yi

- A cewarsa, addini na Allah ne ba nashi ba, kuma Allah zai kare shi tare da sauran kwamandojin kungiyarsa

Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Jama'atu Ahlisunnah Lidda'awati Wal Jihad wacce aka fi sani da Boko Haram, ya yi ikirarin cewa sojoji ba zasu iya kamashi ba saboda aikin Allah yake yi kuma 'Allah zai kare shi'.

Shekau ya bayyana hakan ne a cikin sabon faifan bidiyo mai tsawon minti talatin da ya fitar domin mayar da martani ga rundunar soji, kamar yadda Sahara ta rawaito cewa ta gani a jaridar Humangle.

Shugaban 'yan ta'addar ya fitar da bidiyon ne bayan rundunar soji ta sanar da sabunta farautarsa da wasu kwamandojinsa.

KARANTA: Janar Abubakar Sa'ad ya shigar da karar Buratai, ministan tsaro, da ilahirin rundunar soji

A cikin faifan bidiyon, Shekau ya bayyana a zaune kewaye da wasu muridansa guda biyu a wani daki marar yalwar fili.

Ba zaku iya kamani ba; Shekau ya zolayi sojoji a sabon bidiyo
Shekau a sabon bidiyo @Saharareporters
Asali: Twitter

"Babu wanda zai iya kamani saboda aikin Allah nake yi. Shine zai kareni da sauran masu aiki irin nawa da ke neman kariyarsa.

"Ina da tabbacin cewa Allah zai kare kwamandojina. Aikin Allah muke yi," a cewar Shekau.

A ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamba, rundunar soji ta sanar da sabunta farautar Shekau da sauran manyan kwamandoji a kungiyar Boko Haram.

KARANTA: 'Yan bindiga sun sace ASP 12 daga tawagar 'yan sanda a tsakanin Katsina-Zamfara

A cikin sabon faifan bidiyon, Shekau ya amsa tambayoyi, inda ya ci al washin cewa ko ya mutu yakin Boko Haram ba zai kare ba.

"Kamani ko kasheni ba zai dakatar da aikin ba, addinin ba nawa bane, na Allah ne, ku daina samun rudani," a cewarsa.

Kazalika, Shekau ya yi tir da wasu kwamandojinsa da suka mika wuya ga shirin gwamnati na karbar tuban wadanda suka ajiye makamansu.

"Sun bar hanyar addini," a cewar Shekau, yayin da yake magana a kan irin wadannan kwamandoji.

Kafin ya kalkale bidiyon, Shekau ya zolayi rundunar soji a kan yawan fadawa jama'a cewa ya mutu duk da yana raye.

Kazalika, ya alakanta wahalar da ake ciki a Najeriya da yakar Boko Haram da mambobinta da gwamnati ke yi.

A baya Legit.ng Hausa ta rawaito cewa kwamanda a rundunar soji ya yanke jiki ya fadi matacce yayin da ya ke tsaka da gabatar jawabi ga sojoji a wurin bayar da horo a kan yaki da Boko Haram a jihar Borno.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel