Magidanci ya yi garkuwa da diyarsa a Kano, ya bukaci matarsa ta biya N2m kudin fansa

Magidanci ya yi garkuwa da diyarsa a Kano, ya bukaci matarsa ta biya N2m kudin fansa

- Hausawa kan ce 'in da ranka ka sha kallo' na abubuwa iri daban-daban

- A yayin da ake korafi da cece-kuce a kan yadda masu garkuwa da mutane suka addabi arewa, wani mahaifi a Kano ya ce diyarsa ta cikinsa

- Bayan ya yi garkuwa da ita, ya kira matarsa tare da neman ta gaggauta biyan kudin fansa N2m ko kuma a kashe diyarta

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama tare da gurfanar da wani magidanci, Fahad Ali, bisa zarginsa da yin garkuwa da diyarsa, mai shekaru hudu, tare da neman N2m a matsayin kudin fansarta daga wurin matarsa, mahaifiyar yarinyar.

Dan sanda mai gabatar da kara ya sanar da kotun majistare da ke sansanin alhazai cewa mahaifiyar yarinyar ce ta fara sanar da rundunar 'yan sanda cewa an sace diyarta tare da yin garkuwa da ita.

A cewar dan sandan, mahaifiyar yarinyar mai suna Shamsiyya Mohammed ta shaidawa rundunar 'yan sanda cewa wanda ya sace diyarta ya kirata a waya tare da neman miliyan biyu a matsayin kudin fansar diyarta.

KARANTA: Magidanci ya gutsure ƴan-yatsun matarsa uku ta hanyar gantsara mata cizo

Shamsiyya ta ce babu dadewa da sace yarinyar, a ranar 29 ga watan Satumba, ta samu kiran waya tare da sanar da ita cewa ko ta biya kudin fansa miliyan biyu ko kuma a kashe yarinyar.

Magidanci ya yi garkuwa da diyarsa a Kano, ya bukaci matarsa ta biya N2m kudin fansa
Magidanci ya yi garkuwa da diyarsa a Kano, ya bukaci matarsa ta biya N2m kudin fansa @Thecable
Asali: Twitter

Sai dai, bayan rundunar 'yan sanda ta shafe sati biyu ta na gudanar da bincike, ta gano cewa mijin Shamsiyya, Fahad Ali, shine ya yi garkuwa da yarinyar, wacce aka samu tare da shi.

KARANTA: Kano: Mijina ya na tilasta min akan lallai sai na bashi damar shan jinin al'adarta - Matar aure a gaban kotu

Bayan an gama karanta tuhumar da ake yi masa a gaban kotu, Fahad ya ce shi sam bai aikata wani laifi ba.

Alkaliyar da ta saurari shari'ar, Sakina Aminu, ta bayar da umarnin a tsare Fahad a gidan gyaran hali har zuwa ranar, 24 ga watan Nuwamba, da za'a cigaba da sauraron karar.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, 'yar gwagwarmaya; Aisha Yesufu, ta ce "dukkanmu tsinannu ne a Nigeria" yayin da ta ke martani a kan tsine mata a Masallatai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel