Cacar bakin manya: IGP Adamu ya mayar wa da Janar Garba martani
- Manjo Janar Garba Wahab mai ritaya ya zargi babban sifeton 'yan sanda da gazawa wajen jan ragamar rundunar 'yan sanda
- Ba tare da wani bata lokaci ba, IGP Adamu, ta bakin kakakin rundunar 'yan sanda, DCP Frank Mba, ya mayar da martani
- A cikin martanin, IGP Adamu ya zargi Janar Wahab da yin kalamai cikin jahiltar aikin dan sanda
Babban sufetan rundunar ƴansanda na ƙasa, IGP Mohammed Adamu, ya maida martani ga wani tsohon janaral ɗin soja, Garba Wahab, mai ritaya, wanda ya zarge shi da rashin kula da ragamar rundunar ƴansandan.
A wani jawabin maida martani da mai magana da yawun rundunar ƴansanda, DCP Frank Mba, ya sawa hannu kuma ya rabawa manema labarai, Babban Sufetan ya yi watsi da kalaman Wahab, inda yace kalamansa ba dai-dai bane domin kuwa yana kula da ragamar rundunar yadda ya kamata.
Yace Wahab yayi magana cikin rashin sani da kuma rashin fahimtar ayyukan ƴansanda a mulkin siyasa na dimokaraɗiyya.
"Rundunar tana sanar da Manjo Janaral mai ritaya cewar ya saɓa lamba bisa kalaman da ya yi akan babban Sufetan rundunar ƴansanda na ƙasa.
"Janaral Wahab ya yi kalaman ne cikin ƙungurmin jahilci da rashin fahimtar yadda ake tafiyar da ayyuka da kuma al'ada irin ta aikin ƴansanda a dokance. Tsohon soja mai ritaya ya yi magana akan sha'anin da baida masaniya akai, tunda ba huruminsa bane ba.
"Sanin kanmu ne cewar tun bayan da ya zama Babban Sufeton ƴansanda, IGP Mohammed Abubakar Adamu, NPM, mni,ɗansanda ne abin koyi a duniya.
KARANTA: Arzikin gwal din Zamfara ba na gwamnati bane, in ji kwamishina Nurudden Isa
"A watanni uku da suka gabata tun bayan fara jan ragamar rundunar, ya nuna ƙwarewa a fannonin atisaye da kuma nuna misalin a kan yadda jami'ai zasu kasance"
"Zaku iya ganin misalai daga yadda ya ke ƙoƙarin kawo sauye - sauye don inganta ayyukansu, da kuma ɗabbaƙa doka a ayyukan ƴansanda, baya ga ƙoƙarin inganta mu'amalarsu da mutane da kuma kare haƙƙin ƴanƙasa.
"Tabbas ya yi abin a yaba masa musamman lokacin zanga-zangar #EndSARS, duba da yadda jami'ai suka jure hare-hare da hargitsi gami da lalata dukiyoyi ba tare da sun salwantar da rayuwar kowa ba.
"Irin Wannan salo nashi ya nuna ƙwarewarsa da kuma kuma biyayya ga doka da tsarin ƙasar.
"Rundunar ta shawarci jama'a da kada su bari wasu su sauya musu ra'ayi da zancen shifcin gizo.Ta kuma shawarci masu sukar ayyukan hukumar da suke taimakawa mata da shawarwarin da zasu inganta tsaro a ƙasar.
Da fatan Manjo janaral Garba Wahab zai ringa nazarin magana kafin ya furta jama'a su ji"
Legit.ng Hausa ta rawaito cewa a ranar Talata ne wani birgediya janar (mai ritaya), Abubakar Sa'ad, ya shigar da karar ilahirin rundunar soji a gaban kotun ma'aikata (NIC) domin kalubalantar yi masa ritayar dole.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng