Malamai a Kano na son a kafa dokar hukunta masu yi wa addini ɓatanci

Malamai a Kano na son a kafa dokar hukunta masu yi wa addini ɓatanci

- Gammayar malamai ta Jihar Kano sun nemi Majalisar Jihar ta yi doka da zata rika hukunta duk wanda aka samu da laifin batanci

- Gammayar malaman ta ce ta cimma wannan matsayar ne bayan taron da ta yi kuma hakan shine hanyar tabbatar da zaman lafiya a Kano

- Kakakin majalisar jihar, Gafasa, ya ce majalisar na goyon bayan malaman kuma za ta yi iya kokarinta don ganin anyi dokar tare da aiwatar da ita

Gamayyar malaman addinin musulunci a Kano sun yi kira ga Majalisar Jihar ta yi doka ta zata rika hukunta wadanda suka aikata laifin batanci ga addinin musulunci.

Tawagar malaman sun yi wannan kiran ne yayin ziyarar ban girma da suka kai wa kakakin majalisar jihar Kano, Abdulazeez Gafasa.

Malamai a Kano na son a kafa dokar hukunta masu yi wa addini ɓatanci
Malamai a Kano na son a kafa dokar hukunta masu yi wa addini ɓatanci. @thecableng
Asali: Twitter

Da ya ke jawabi yayin ziyarar, mamban gammayar Ibrahim Muazzam ya ce sun amince akwai bukatar kafa doka da zata dinga hukunta yayin lakca kan 'batanci' ga Annabi Muhammad (SAW) da Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya yi.

DUBA WANNAN: 'Yan jam'iyyar APP 20,000 ciki da shugbansu sun koma PDP a Ebonyi

Muazzam ya ce don tabbatar da zaman lafiya a Kano, akwai bukatar a kafa doka da za ta rika hukunta wadanda suka aikata laifin batanci a jihar.

Ya ce gammayar ta zauna don daukan matakan da za su kare afkuwar wani abu da ka iya biyo bayan kalaman da Shugaban Faransa ya furta game da Annabi Muhammad.

"Matsayar mu ta kunshi maye gurbin koyar da harshen faransanci a larabci a dukkan makarantun Kano," in ji shi.

"Musulmi su kauracewa kayayyakin faransa da duk wata harka ta siyasa da su har sai sun durkushe.

"Ya kamata dukkan musulmin duniya su dauki Macron da gwamnatinsa a matsayin wadanda ke asassa muzanta addinin musulunci."

DUBA WANNAN: Saudiyya ta bada guraben karatu 424 kyauta ga ɗaliban Najeriya, ta bayyana yadda za a iya samu

A bangarensa, Kakakin majalisa Gafasa ya ce majalisar tana goyon bayan gammayar inda ya kara da cewa majalisar za tayi dokoki don tabbatar da zaman lafiya a jihar.

"Muna goyon bayan wannan matakin kuma za muyi iya kokarinmu don yin dokar da kuma aiwatar da ita," in ji Gafasa.

"A wuraren da bamu da iko kuma, za mu rubuta wasika ga wadanda alhakin abin ya rataya a kansu."

A wani labarin, bala'i ya afku a jihar Bauchi yayin da wani kwale-kwale mai dauke da mutum 23 don tsallakar dasu gona ya yi sanadiyar mutuwar mutane 18.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakili ne ya bayyana haka a ranar Juma'a 13 ga watan Nuwamba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel