An kama mai garkuwa da mutanen da ya kashe 'yar shekara 8 bayan ya karbi N500,000 a Kano

An kama mai garkuwa da mutanen da ya kashe 'yar shekara 8 bayan ya karbi N500,000 a Kano

- Ya yi garkuwa tare da kashe yarinya yar shekara 8 bayan ya karbi kudin fansa

- Ya kashe kudin fansar da ya kai Naira 500,000 a karuwanci da cha-cha

- Lamarin ya faru tun 5 ga watan Yuni amma wanda ake zargin bai shiga hannu ba sai 7 ga watan Nuwamba

Rundunar yan sandan Jihar Kano ta ce ta kama wani mai garkuwa da mutane Habibu Sale mai shekara 24, wanda ya yi garkuwa da kashe yarinya yar shekara takwas, Asiya Tasiu a kauyen Chikawa, a karamar hukumar Gabasawa da ke jihar.

Mai magana da yawun rundunar, Abdullahi Haruna ne ya bayyana haka ranar Talata yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano, ya ce wanda ake zargin ya kashe wadda ya yi garkuwar da ita bayan biyan kudin fansar Naira 500,000.

Yan sanda sun kama mai garkuwa da mutanen da ya kashe yaro bayan an biya su kudin fansa
Yan sanda sun kama mai garkuwa da mutanen da ya kashe yaro bayan an biya su kudin fansa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yan jam'iyyar APP 20,000 ciki da shugbansu sun koma PDP a Ebonyi

Da yake magana a madadin kwamishina, Habu Sani, mai magana da yawun rundunar ya ce lamarin ya faru 5 ga watan Yuni, amma yan sanda sun sami nasarar kama shi ranar 7 ga Nuwamba.

Binciken yan sanda, a cewar kakakin, ya gano cewa, "Mal Sale ya kashe yarinyar bayan karbar kudin fansa kuma ya binne ta a bayan garin Chikawa don boye laifin sa, saboda suna zaune a unguwa daya da wadda ya sace din, don tsoron kada ta gane shi kuma ta tona masa asiri."

Duk da cewa Mal. Sale ya ce shi kadai ya aikata laifin, yan sanda sun bayyana cewa dole akwai wasu, saboda ya ce ya kashe kudin fansar da ya kai Naira 500,000 a shan miyagun kwayoyi da karuwai da cha-cha.

KU KARANTA: Buhari na buƙatar goyon baya don magance sheɗanun da ke Najeriya, in ji Tambuwal

"Bayan na karbi kudin, na tafi Kaduna inda muka more kudin dani da abokai na," a cewar wanda ake zargin.

Ya kuma bayyana cewa yarinyar ta rasu sanadiyar hadarin babur lokacin da yake yunkurin kai ta maboyarsa.

A wani labarin, bala'i ya afku a jihar Bauchi yayin da wani kwale-kwale mai dauke da mutum 23 don tsallakar dasu gona ya yi sanadiyar mutuwar mutane 18.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakili ne ya bayyana haka a ranar Juma'a 13 ga watan Nuwamba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel