Yanzu-yanzu: Mayakan Boko Haram sun harbo jirgin sama a Borno
- Labari da duminsa da ke isowa a yanzu shine harbo jirgin sama da mayakan Boko Haram suka yi
- An gano cewa jirgin saman mallakin gwamnatin jamhuriyar Nijar ne kuma yana dauke da fasinjoji
- Duk da mutane biyar ne suka rasa rayukansu, hukumar sojin Najeriya na bincike a kan lamarin
Wasu wadanda ake zargin 'yan Boko Haram ne sun harbo jirgin sama dauke da mutanen da har yanzu ba a san ko su waye ba a karamar hukumar Bama ta jihar Borno.
Jaridar Daily Trust ta gano cewa lamarin ya auku ne a kusa da garin Banki wurin karfe 10 na safiyar Talata.
An gano cewa a kalla mutum 5 ne suka rasa rayukansu sakamakon harbo jirgin saman da aka yi.
KU KARANTA: Dakarun sojin saman Najeriya sun ragargaza sansanin 'yan Boko Haram a Sambisa
Wata majiyar gaggawa daga Banki wacce ta ziyarci wurin da lamarin ya faru tare da sojin Najeriya, ta ce mayakan ta'addanci ake zargi da baro jirgin da ya kasance mallakin gwamnatin Nijar.
Har yanzu hukumar sojin Najeriya basu tabbatar da aukuwar lamarin ba.
Karin bayani na nan tafe...
KU KARANTA: Obasanjo zai nufi kasar Ethiopia domin aiwatar da wani babban al'amari
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng