Ruhi mai tsarki: Miji ya saki matarsa saboda ta hana ya sadu da ita

Ruhi mai tsarki: Miji ya saki matarsa saboda ta hana ya sadu da ita

- Miji ya nemi a raba auransu da matarsa saboda ta hana ya yi mu'amalar aure da ita

- A cewar mijin, fasto din matarsa ne ya hana ta tara da shi saboda wai tana dauke da cikin ruhi mai tsarki

- Ya zargi matarsa da jin maganar fasto din fiye da nashi duk da cewar a karkashinsa ta ke

Wani magidanci da ya gaji da halin matarsa na hana masa hakkinsa na auratayya bisa hujjar cewa tana dauke da cikin ruhi mai tsarki, ya nemi a raba aurensu.

Mutumin wanda ya kasance dan kasar Zambiya ya yi ikirarin cewa tun watan Yuli rabon da matarsa ta bari ya kusanceta da sunan auratayya.

KU KARANTA KUMA: Da zafinsa: Sojoji sun yi ƙulin ƙulin Kubura da mayaƙan Boko Haram a Sambisa

Ruhi mai tsarki: Miji ya saki matarsa saboda ta hana ya sadu da ita
Ruhi mai tsarki: Miji ya saki matarsa saboda ta hana ya sadu da ita Hoto: @THISDAYLIVE
Asali: Twitter

Ya ce tana hana shi hakkinsa saboda wani manzo na coci da take tuntuba tun a shekarar 2018 ya fada mata cewa kada ta yarda ta hada gado dani domin tana dauke da cikin ruhi mai tsarki wanda ake kira da “Holy Spirit” a turance, jaridar The Nation ta ruwaito.

mutumin ya yi zargin cewa matarsa mai shekaru 38, ta fi jin maganar limamin cocin fiye da nashi, sannan cewa a duk lokacin da ya nemi hakkinsa na aure sai ta tuntube shi.

KU KARANTA KUMA: Ikon Allah sai kallo: Bidiyon wani mutum yana rabon fada tsakanin kaji biyu

A gefe guda, wani al'amari mai firgitarwa ya faru a jihar Benue, inda wani Nicodemus Nomyange, mai shekaru 40 da haihuwa, ya banka wa kansa da budurwarsa, Shinnenge Pam, wuta, a anguwar Inikpi.

The Nation ta ruwaito yadda Nomyange, wanda yake da yara kuma ya jima yana soyayya da Pam na wani lokaci, ya bukaci aurenta.

Rahotanni sun nuna yadda Pam ta watsa masa kasa a ido, inda ta ki amince da tayin aurensa, a cewarta ta gwammaci auren mutumin da bai taba aure ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng