Da zafinsa: Sojoji sun yi ƙulin ƙulin Kubura da mayaƙan Boko Haram a Sambisa

Da zafinsa: Sojoji sun yi ƙulin ƙulin Kubura da mayaƙan Boko Haram a Sambisa

- Dakarun sojojin Najeriya na Operation Lafiya Dole sun kashe yan ta’addan Boko Haram, kamar yadda John Enenche ya bayyana

- Tawagar rundunar sojin sama ne suka gudanar da harin wanda ya yi sanadiyar mutuwar yan ta’adda a yankin Sambisa

- Wannan ya kasance daya daga cikin nasarorin da aka samu na hadin gwiwa a kokarin da ake na kawo karshen fashi da makami da ta’addanci a kasar

An kaddamar da wani gagarumin hari a kan yan ta’addan Boko Haram a jihar Borno bayan jami’an rundunar sojin sama na Operation Lafiya Dole sun kashe da dama daga cikinsu.

A cewar wata sanarwa da Manjo Janar John Enenche, jagoran labarai na rundunar tsaro ya saki a ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamba, dakarun sojin sun kashe yan ta’addan a wasu hare-hare da suka kai masu ta sama.

Enenche ya bayyana cewa harin, wanda aka aiwatar a ranar Asabar, 14 ga watan Nuwamba, a Gobara da yankin Sambisa, ya gano yadda aka lalata kayayyakin yan ta’addan.

KU KARANTA KUMA: Da ɗuminsa: Atiku Abubakar ya miƙa ƙoƙon bara ga mambobin PDP na shiyyar Kudu kan zaben 2023

Da zafinsa: Sojoji sun yi ƙulin ƙulin Kubura da mayaƙan Boko Haram a Sambisa
Da zafinsa: Sojoji sun yi ƙulin ƙulin Kubura da mayaƙan Boko Haram a Sambisa Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa an gano yan ta’addan a karkashin ciyayi da ke wajen, inda jiragen sojin suka kai hari kai tsaye wanda ya yi sanadiyar mutuwar wasu daga cikin yan ta’addan.

Enenche ya ce rundunar sojin Najeriya ta jajirce domin kawo karshen matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta sannan ya yi kira ga basu goyon baya a yaki da yan ta’adda da wasu miyagu da ke tayar da zaune tsaye a kasar.

KU KARANTA KUMA: Rabon kwado: Gwamna Inuwa Yahaya ya ba wanda ya yi wa Buhari tattaki kyautar mota da N2m

A wani labarin, mun ji cewa da yammacin Litinin ne yan bindiga suka yi garkuwa da wasu ma'aikatan hukumar tara kudaden shiga ta Benue a karamar hukumar Vandeikiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel