'Yan bindiga cikin kakin soji sun yi garkuwa da ma'aikatan hukumar haraji 5

'Yan bindiga cikin kakin soji sun yi garkuwa da ma'aikatan hukumar haraji 5

- Yan bindiga sun mamaye shingen binciken hukumar haraji ta jihar Benue tare da yin garkuwa da ma'aikatan hukumar su biyar

- Har yanzu ba a san inda ma'aikatan suke ba duk kuwa da korafi da aka kai wa runudnar 'yan sanda

- Har yanzu ba a ji ta bakin rundunar 'yan sandan jihar akan wannan al'amari ba

Da yammacin Litinin ne yan bindiga suka yi garkuwa da wasu ma'aikatan hukumar tara kudaden shiga ta jihar Benue a karamar hukumar Vandeikiya da ke jihar.

Da yake shaidawa manema labarai, mai magana da yawun shugaban hukumar, Ati Terkula, ya ce lamarin ya faru da misalin 6:30 na yamma kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Yan bindiga sanya da kayan sojoji sun sace ma'akatan tattara haraji biyar
Yan bindiga sanya da kayan sojoji sun sace ma'akatan tattara haraji biyar. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun sace ɗaliban ABU Zaria 17 a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Terkula ya ce, "yan bindigar sun kai hari shingen hukumar dake karamar hukumar Vandeikiya, suka lalata kayayyaki da kuma garkuwa da ma'aikata biyar da suke aiki a lokacin.

"Yan bindigar sun yi shiga cikin kayan sojoji cikin wata mota kirar Hilux da babura uku. Suka mamaye sansanin binciken hukumar a Vandeikiya, suka kona baburan ma'aikata, harbi kan mai uwa da wabi, kuma suka yi garkuwa da wasu ma'aikatan hukumar tara kudaden shiga biyar da raunata wasu da dama.

KU KARANTA: Hadimin Ganduje ya rabawa matasa tallafin jakuna a Kano (Hotuna)

"A halin yanzu, ba a san inda ma'aikatan suke ba, duk kuwa da cewa an kai korafi ga ofishin yan sanda na Vandeikiya.

"Kokarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, DSP Catherine Anene, ya ci tura saboda an kasa samun wayar ta."

A wani labarin, bala'i ya afku a jihar Bauchi yayin da wani kwale-kwale mai dauke da mutum 23 don tsallakar dasu gona ya yi sanadiyar mutuwar mutane 18.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakili ne ya bayyana haka a ranar Juma'a 13 ga watan Nuwamba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel