A matsayinku na Shugabanni kun yi kasa a gwiwa – CNG ga Gwamnoni, Buhari

A matsayinku na Shugabanni kun yi kasa a gwiwa – CNG ga Gwamnoni, Buhari

- Kungiyar CNG ta yi kaca-kaca da shugabannin da ke mulki a kasar nan

- CNG ta ce Gwamnonin jihohi da Gwamnatin Tarayya sun gaza kawo gyara

- Wannan shi ne ra’ayin wasu manyan Ibo da ke zaune a Arewacin Najeriya

Gamayyar kungiyoyin Arewa (CNG) da wata kungiya ta shugabannin Ibo da ke Arewacin Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu game da shugabannin kasar nan.

A taronsu, CNG da Igbo Community Leaders of Northern Nigeria sun yi ittifakin shugabannin Najeriya sun gagara hada kan al’umma da kawo cigaban kasa.

Vanguard ta ce kungiyoyin sun bayyana wannan ne a karshen zaman da su ka yi a Abuja, inda su ka fitar da jawabi cewa duka shugabanni masu-ci a yau, sun gaza.

KU KARANTA: Kwamitin binciken Salami ba zai yi wa Magu adalci ba – Kungiyoyi

Kungiyoyin ta bakin shugabannin da su ka yi magana a madadinsu, sun fitar da wannan matsaya ne ba tare da la’akari da jam’iyyun siyasan shugabannin nan ba.

CNG da takwararta sun yi magana game da salon nadin mukaman gwamnatin tarayya ta Muhammadu Buhari da kuma kawo ayyukan da za su taimaki kasa.

Wadannan kungiyoyi sun fitar da jawabi ne ta bakin Mai magana da yawun bakin CNG, Abdul-Azeez Suleiman, da sakataren kungiyar Ibon, Austin Ifedinezi.

Jawabin kungiyoyin ya yi kiran a rika tafiya da duka kabilun Najeriya wajen gudanar da mulki.

KU KARANTA: Yajin aiki: ASUU ta karyata Minista, ta ce da sauran jan aiki a kasa

A matsayinku na Shugabanni kun yi kasa a gwiwa – CNG ga Gwamnoni, Buhari
Shugaban kasa Buhari Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

A wajen wannan taron har wa yau, kungiyoyin sun koka game da yadda sha’anin tsaro ya ke dada tabarbare wa, tare da bada shawarwarin da zai ceci al’ummar kasar.

A karshe, kungiyoyin Arewan sun yi Allah-wadai da yadda wasu su ka yi amfani da zanga-zangar lumanar #EndSARS wajen yin ta’adi a wasu bangarorin Najeriya.

Mun samu rahoto cewa shugabannin APC na shirin yi wa jam'iyyar PDP farat-daya a wasu jihohin da ta ke ji da su a cikin yankin Kudu maso gabashin Najeriya.

APC ta fara kokarin janye Gwamnoni da ‘Yan Majalisar hamayya domin yi wa 'yan adawa lahani.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng