Umahi: Jam’iyyar APC ta na neman jawo Ugwuanyi, Ikpeazu da Obiano

Umahi: Jam’iyyar APC ta na neman jawo Ugwuanyi, Ikpeazu da Obiano

- Jam’iyyar APC ta na zawarcin Jagororin adawa a shiyyar Kudu maso gabas

- Mai Mala Buni ya umarci ‘Yan APC su karkato da wasu Gwamnonin yankin

- APC ta na sa ran samun karin Gwamnoni da ‘Yan Majalisa kafin zaben 2023

Jaridar Punch ta ce jam’iyyar APC ta na hobbasa na ganin ta jawo hankalin wasu gwamnonin hamayya a yankin Kudu maso gabashin Najeriya.

Jam’iyyar APC mai mulki ta na zawarcin kusoshin adawar ne bayan maganar sauya-shekar gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi daga PDP.

Shugabannin rikon-kwaryan jam’iyyar APC, sun ba manyanta a kudu maso gabashin Najeriya umarni su karkato da hanlin manyan ‘yan hamayya.

KU KARANTA: PDP ta rude, za ta yi zaman gaggawa bayan ta ji Umahi zai sauya-sheka

APC a karkashin jagorancin Mai Mala Buni ta na neman samun karin yawan rinjaye a majalisar tarayya da iko a jihohi a yankin da PDP ta ke da karfi.

Daga cikin wadanda shugabannin APC su ke hari akwai gwamnan jihar Anambra, Willy Obiano da takwarorinsa Okezie Ikpeazu da Ifeanyi Ugwuanyi.

Jam’iyyar PDP ta fada wa jaridar cewa yunkurin ‘ya ‘yan APC ba ya tada mata hankali domin kuwa a karkashin PDP aka zabi wadannan gwamnoni.

PDP mai hamayya ta na ganin cewa nan ba da dadewa ba za a samu sauyin-sheka a jirgin APC.

KU KARANTA: Kungiya ta caccaki Gwamnonin Ibo saboda yin gum da kisan Musulmai

Umahi: Jam’iyyar APC ta na neman jawo Ugwuanyi, Ikpeazu da Obiano
Gwamnonin Kudu maso gabas Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Masu yi wa APC wannan kokari na rusa jam’iyyar PDP sun hada da gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodimma, Uzor Kalu da kuma Rochas Okorocha.

Wannan ya na cikin shirin da APC ta ke yi na ganin ta samu kuri’u masu tsoka a zabe mai zuwa na 2023.

Jigon APC a Kudancin Najeriya, Orji Uzor Kalu, ya bayyana sha’awar zuba kudi domin farfado da Arsenal ta yadda za ta lashe gasar kofin Ingila da Turai.

Tsohon Gwamnan ya yunkuro, ya na neman zuba jari a Arsenal bayan ya yi nasara da Enyimba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng