Duba hotunan tsuntsu mai suna New Kim da aka siyar a kan N729 miliyan

Duba hotunan tsuntsu mai suna New Kim da aka siyar a kan N729 miliyan

- Tseren tsuntsaye yana daya daga cikin wasanni a kasar Belgium

- Masu siyar da tsuntsayen tseren suna ta samun dumbin dukiya

- Ana sayar da tsuntsu mai shekaru 2, a kalla N729,479,670.40

An sayar wa wani dan kasar China da wata tsuntsuwa wacce suke kira New Kim a ranar Lahadi.

A kasar Belgium, ana sayar da tsuntsuwar tsere, wacce suke kira da New Kim a kalla euros miliyan 1.6, wanda yayi daidai da N729,479,670.40.

Wani babban dan kasuwa mai harkokin tsuntsaye ya siyar da tsuntsun a wani taro da aka yi ranar Lahadi, 15 ga watan Nuwamba, kamar yadda Indian Express suka ruwaito.

Shugaban kungiyar sayar da tsuntsayen, Pascal Bodengien, ya ce mutane su na tururuwar zuwa siyan tsuntsaye a wurinsu.

Bodengien ya yi na'am da babban cigaban da suka samu na siyar da tsuntsu daya a euro miliyan 1.6, ya kuma ja kunnen masu son shiga harkar wasan don samun kudi su sabunta tunaninsu.

KU KARANTA: Shugabancin kasa a 2023: PDP na fuskantar babban kalubale a kudu maso gabas

Duba hotunan tsuntsu mai suna New Kim da aka siyar a kan N729 miliyan
Duba hotunan tsuntsu mai suna New Kim da aka siyar a kan N729 miliyan. Hoto dagaTNT, Reuters
Asali: UGC

KU KARANTA: Bidiyon Aku a wata liyafa, yana kwasar wata rawa mai bada mamaki

A wani labari na daban, Ali Ndume, sanata mai wakiltar kudancin Borno, ya ce da yawa daga cikin wadanda suke karkasin shugaban kasa Muhammadu Buhari barayi ne.

A ranar Lahadi, gidan talabijin din Channels sun yi hira da sanatan inda ya sanar da hakan, ya ce akwai mutanen da suke kokarin ganin bayan cigaba a mulkinsa.

Bayan an tambayeshi a kan yadda mulkin APC yake tafiya, cewa yayi gaskiya ba ya farinciki da tafiyar ta shekaru 5. Duk da suna yin iyakar kokarinsu, amma akwai gurabe da dama da ya kamata a cike.

A cewarsa, duk da kokarinsu, sai mutane sun zagesu, jaridar The Cable ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng