An kama kansila kan zargin yi wa matar yayansa duka

An kama kansila kan zargin yi wa matar yayansa duka

- Ƴan sanda sun tsare Blackson Etche da ake zargi da yi wa matar yayansa, Love, duka

- Blackson ya amsa gayyatar da ƴan sanda suka yi masa inda suka tsare shi don cigaba da bincike

- Blackson ya musanta cewa ya doki matar yayansa, Love, don haka ƴan sanda suka bukaci a gayyato ƴan uwansa mata don su bada ba'asi

Rundunar ƴan sandan Jihar Rivers ta ce ta kama Kansila a majalisar Etche, Blackson Nwanyawu kan zargin yi wa matar yayansa duka.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Nnamdi Omoni, ya sanar da wakilin The Punch a ranar Litinin cewa an tsare Blackson bayan ya kawo kansa ofishin ƴan sanda bayan gayyatarsa.

An kama kansila kan zargin yi wa matar yayansa duka
An kama kansila kan zargin yi wa matar yayansa duka. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Tunda farko, Legit.ng ta ruwaito cewa wacce abin ya faru da ita, Love Nwanyawu, ta zargi Blackson, wanda shine shugaban majalisar Etche, da wasu mutane da yi mata rauni bayan zargin ta da maita.

DUBA WANNAN: Dan ƙwallon Najeriya ya rasu bayan ya yanke jiki ya faɗi a yayin buga wasa a Abeokuta

Love ta yi korafi game da lamarin a ofishin kare hakkin bil adama na rundunar ƴan sanda.

Omoni, kansilar, ya musanta cewa ya yi wa matar dan uwansa duka.

Ya ce, "Blackson yana tare da mu don amsa gayyatar mu. Ya yi jawabi ya musanta cewa ya doki matar. Mun ce ya kira ƴan uwansa mata da suma an ambace su a cikin lamarin.

"Don haka, har yanzu muna kan bincike. Yana tsare muna masa tambayoyi. Ya musanta zargin, za muyi ƙoƙarin tabbatar da ingancin abinda muke zarginsa daga ƙarshe doka za tayi halinta."

KU KARANTA: Hadimin Ganduje ya rabawa matasa tallafin jakuna a Kano (Hotuna)

Omoni ya ce wacce abin ya faru da ita tana asibiti tana karɓar magani kuma muna kira ga dukkan iyalan su zauna lafiya su bari ƴan sanda ta yi bincike.

A wani labarin, bala'i ya afku a jihar Bauchi yayin da wani kwale-kwale mai dauke da mutum 23 don tsallakar dasu gona ya yi sanadiyar mutuwar mutane 18.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakili ne ya bayyana haka a ranar Juma'a 13 ga watan Nuwamba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel