Hadimin Ganduje ya rabawa matasa tallafin jakuna a Kano (Hotuna)

Hadimin Ganduje ya rabawa matasa tallafin jakuna a Kano (Hotuna)

- An saka jaki ne saboda daya daga cikin wanda zasu amfana da tallafin ya bukaci hakan

- An raba wasu kayayyaki da dama kamar babura da kwanukan rufi da bulon gini

- Jiga jigan ma'aikatar matasa sun halarci taron da ya gudana a harabar ma'aikatar a ranar Alhamis

Mataimaki na musamman ga gwamna Ganduje akan harkokin ci gaban matasa, Murtala Gwarmai a ranar Alhamis 12 ga watan Nuwamba ya rabawa matasa jakuna da sauran kayayyaki don tallafa musu.

The Cable ta ruwaito cewa matasan da ba su gaza arba'in ba a fadin jihar ne suka amfana a taron da ya gudana a harabar ma'aikatar matasa da wasanni.

Hadimin Ganduje ya rabawa matasa jaki da sauran kayayyaki don tallafa musu
Hadimin Ganduje ya rabawa matasa jaki da sauran kayayyaki don tallafa musu. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sarkin Saudiyya ya kira Buhari ta waya sun tattauna

Gwarmai ya kuma raba babura, kudade kimanin 100,000, bulon gini da kuma kwanon rufi da ma wasu da dama, yace dalilin da yasa aka saka jaki shine, daya daga cikin wanda za su amfana da tallafin ne ya bukaci a bashi saboda yana amfani dashi wajen safarar yashi, dutse da bulo, kuma yace zai taimaka masa wajen bunkasa kasuwancin sa.

Hadimin Ganduje ya rabawa matasa jaki da sauran kayayyaki don tallafa musu
Hadimin Ganduje ya rabawa matasa jaki da sauran kayayyaki don tallafa musu. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Wasu mazauna Kaduna sun soki harajin cigaba na N1,000 da gwamnati ta sakawa duk baligai

Wanda suka halarci taron sun hada da kwamishinan matasa da wasanni, Kabiru Ado Lakwaya, babban mai bada shawara kan harkokin matasa II Ibrahim Ahmad da sauran jiga jigan ma'aikatar.

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, wasu magidanta a karamar hukumar Ganjuwa ta Jihar Bauchi sun koka kan karancin kororon roba a yankin wadda ke taimaka musu wurin bada tazarar haihuwa.

The Punch ta ruwaito cewa shugaban kwamitin Cibiyar Lafiya ta mazabar Kafin Madaki, Mustapha Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin da ya yi wa manema labarai jawabi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164