Jam’iyyar PDP na shirin yin taro a dalilin yunkurin sauya-shekar Dave Umahi

Jam’iyyar PDP na shirin yin taro a dalilin yunkurin sauya-shekar Dave Umahi

- Jam’iyyar PDP ta shiga wani yanayi na kidimewa a halin yanzu

- Ana rade-radin Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi zai koma APC

- Babbar Jam’iyyar hamayyar za ta hana Gwamnan sauya-sheka

Rahotanni sun bayyana cewa uwar jam’iyyar PDP ta kira wani taro na gaggawa a dalilin sauyin-shekar da ake zargin gwamnan Ebonyi zai yi.

NWC ta kira taron majalisar zartarwa, NEC domin ganin yadda za a dakile yunkurin gwamna Dave Umahi na ficewa daga PDP, ya koma APC.

Jaridar This Day ta ce ana sa ran za ayi wannan zama ne a ranar Alhamis, 19 ga watan Nuwamba.

KU KARANTA: Mun amince da komawar Gwamna Ebonyi APC - Kungiya

Za ayi wannan taro na gaggawa ne a sakatariyar jam’iyyar da ke babban birnin tarayya Abuja.

Haka zalika shugabannin kwamitin amintattu na jam’iyyar watau BOT za su yi wani zama a wannan wuri game da lamarin a ranar Larabar nan.

Ana sa ran shugabannin PDP za su yi amfani da wannan dama wajen shawo kan gwamnan, ta yadda za su hana shi sauya-sheka zuwa APC mai mulki.

Gwamna Dave Umahi ya na cikin kusoshin jam’iyyar PDP, ana tunanin cewa ya na harin tikitin takarar shugaban kasa ne a zabe mai zuwa na 2023.

KU KARANTA: Ana rade-radin Gwamnan Ebonyi David Umahi zai sauya-sheka

Jam’iyyar PDP na shirin yin taro a dalilin yunkurin sauya-shekar Dave Umahi
Gwamna Dave Umahi Hoto: www.thecable.ng
Asali: UGC

Jim kadan bayan rade-radin gwamnan na Ebonyi zai bar PDP, sai aka ji labarin cewa wani daga cikin kwamishinoninsa, Lazarus Ogbee ya ajiye aiki.

Jam’iyyar APC ta reshen jihar Ebonyi ta tabbatar da cewa akwai maganar sauyin-shekar gwamnan, Umahi ya na gana wa da manyan APC na kasa.

Kwanakin baya kun ji gwamnan Jihar Ebonyi ya shaida wa shugabannin jam'iyyar PDP cewa zai fice daga jam'iyyar, ya tattara ya koma APC mai mulki.

Amma gwamnan ya bayyana zai iya tsaya wa a jam'iyyar ta PDP matukar za a ba Ibo tuta a 2023.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel