Makusanta shugaban kasa su na amfani da biyan tallafin man fetur don azurta kansu - Shugaban NNPC

Makusanta shugaban kasa su na amfani da biyan tallafin man fetur don azurta kansu - Shugaban NNPC

- Gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta janye tallafin man fetur gaba dayansa

- Ana zaton cewa shugaban hukumar harkar man fetur na Najeriya (NNPC), Mele Kyari, ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo karshen biyan tallafin mai

- A wata hira da aka yi da shi a wani gidan Radiyo da ke Kaduna, Kyari ya bayyana cewa an janye tallafin ne saboda kwalliya ta gaza biyan kudin sabulu

Mele Kyari, shugaban hukumar harkar man fetur ta Najeriya (NNPC), ya ce makusanta shugaban kasa ne su ka ci moriyar tallafin man fetur sabanin talakawan Najeriya da ake fitar da kudin tallafin dominsu.

Jaridar TheCable ta rawaito cewa Kyari ya bayyana hakan ne ranar Lahadi yayin wata hira da aka yi da shi cikin harshen Hausa a gidan radiyon Liberty FM da ke garin Kaduna.

Kyari ya bayyana cewa an cire tallafin ne saboda amfani da ake da kudaden da ake warewa wajen tafka almundahana da wasoson dukiyar kasa wacce ya kamata kowa ya amfana.

Ya bayyana cewa talaka ba ya cin moriyar kudin tallafin man fetur da gwamnati ke fitarwa duk da saboda talakawa ake fitar da makudan kudaden.

A cewar Kyari, cire tallafin mai gaba daya zai bawa gwamnati damar yin amfani da kudadenta wajen samar da wasu abubuwan more rayuwa da yin wasu sauran muhimman aiyuka da za su amfani dukkan 'yan kasa.

DUBA WANNAN: Sunayensu: Hameed Ali ya nada DCGs 2, ACGs 5, ya sauya wa manyan jami'ai 5 wurin aiki

"Farashin danyen man fetur ba boyayyen abu bane, kowa zai iya lissafi ya san nawa za a kashe domin sayo fetur daga kasuwar duniya, amma tun da aka fara shigo da man fetur gwamnati ta ke bayar da tallafi saboda talaka ya siyeshi da araha a cikin gida.

Makusanta shugaban kasa su na amfani da biyan tallafin man fetur don azurta kansu - Shugaban NNPC
Dangote da Mele Kyari
Asali: UGC

"Manufar bayar da tallafin man fetur shine domin ya amfani 'yan Najeriya, wannan ita ce niyyar gwamnati. Amma a zahiri ba jama'ar ne suke cin moriyarsa ba. Ba talakawane suka mallaki gidajen man fetur ba, ba kuma sune suke yin kasuwancin mai ba.

"Tallafin man fetur da gwamnati ta shafe shekaru ta na bayarwa shine tushen duk wata badakala da cin hanci da ake fama dasu a kasar nan.

DUBA WANNAN: Mamba a majalisar wakilai ya koma APC bayan gwamnan PDP ya fada ma sa bakar magana

"Alal misali, idan aka duba daga shekarar 2006 zuwa 2020, mun kashe fiye da tiriliyan N10 a kan biyan tallafin man fetur.

"Bayan tallafin man fetur, gwamnati ta na bayar da tallafi a kan kudaden kasar waje, kowa ya san farashin dala a kasuwa, amma duk da haka gwamnati ta ke biyan tallafi don ta yi sauki. Gwamnati ta kashe tsakanin tiriliyan N14 zuwa tiriliyan N15 daga 2006 zuwa 2020.

"Ba talakawan Najeriya ne suke cin moriyar duk wadannan tallafi ba, wasu 'yan tsiraru ne da ke da kusanci da shugaba, kuma duk attajirai ne ma su karfi. Su na kara azurta kansu da kudaden da ake biya domin morewa da jin dadin talaka," a cewar Kyari.

Kyari ya bayyana cewa gwamnati za ta yi amfani da kudin tallafin mai da ta janye wajen yin wasu muhimman aiyukan da za su kawowa kasa cigaba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel