Wata mata sanye da hijabi ta yi garkuwa da wani yaro a Jigawa
- Wata mata da ake zaton mai garkuwa da mutane ce ta badda kammani sanye da hijabi, sannan ta sace wani yaro a jihar Jigawa
- Rundunar yan sandan Jigawa ta tabbatar da faruwar lamarin
- An tattaro cewa masu garkuwa da mutanen sun saki yaron bayan mahaifinsa ya biya kudin fansa
Hankula sun tashi a jihar Jigawa lokacin da wata mata sanye da hijabi ta yi garkuwa da wani yaro dan shekara biyar mai suna Muhmad Tasiu, a Dutse, babbar birnin jihar.
Shaidu sun bayyana cewa yaron ya bata a ranar Lahadi, 15 ga watan Nuwamba, jim kadan bayan an gan shi tare da wata mata da ba a san ko wacece ba, jaridar Premium Times ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Ba fa a mulkin soja muke ba; Buba Galadima ya kwankwashi Buhari a kan taba jagororin ENDSARS

Asali: UGC
Kakakin yan sandan jihar, Audu Jinjiri ya ce lamarin garkuwan ya afku ne a garin Galamawa.
Rundunar yan sandan ta ce:
“Daga bisani masu garkuwa da mutanen sun kira iyayensa inda suka bukaci a biya kudin fansa domin su saki yaron.”
An tattaro cewa mahaifin yaron ya biya kudin fansa naira miliyan 1 domin a saki dan nasa.
Sai dai, rundunar yan sandan ta ce bata san da cewar an biya kudin fansa kafin sakin yaron ba.
KU KARANTA KUMA: Ilimin ƴaƴa mata: Hankalin Sarakunan Arewa ya tashi kan wasu jihohi 5
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Katsina, Bello Masari, a ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamba, ya koka kan ayyukan yan bindiga a jiharsa.
Masari, wanda ya yi magana da manema labarai a Kafur ya bayyana cewa mafi akasarin wadannan miyagun su kan je su haddasa tashin hankali a Katsina sannan su koma mabuyarsu a Zamfara, jaridar The Nation ta ruwaito.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng