Malami ne ya hana a taso da keyar Diezani ta dawo Najeriya ba ni ba – inji Magu

Malami ne ya hana a taso da keyar Diezani ta dawo Najeriya ba ni ba – inji Magu

Tsohon shugaban hukumar EFCC da aka dakatar, Ibrahim Magu, ya yi raddi game da zargin da ake jifarsa da su, daga ciki har da kawo matsala a shari’ar Diezani Alison-Madueke.

Ana zargin Ibrahim Magu da hannu wajen bata yunkurin gwamnatin Najeriya na dawo da Diezani Alison-Madueke da wasu da ake zargi da laifin sata domin ayi masu shari’a.

Mista Ibrahim Magu ya musanya wannan zargi, ya maida laifin kan mai zargin na sa watau ministan harkar shari’a na kasa, Abubakar Malami, ya ce laifin sa ne ba na hukumar sa ba.

Kamar yadda NAN ta bayyana, ministan ya zargi Magu da kin hada-kai da hukumomin kasar Ingila da ke binciken rashin gaskiyar tsohuwar minister man Najeriya, Alison-Madueke.

A martanin da tsohon shugaban na EFCC ya bada, ya karyata maganar cewa ya hana hukumar NCA wasu bayanai. Labarin martanin ya fito ne daga jaridar Premium Times a ranar Talata.

A cewar Magu NCA ta na aiki da hukumar EFCC tare kuma har su kan ba su wasu bayanan sirri da su ka shafi binciken Diezani Allison-Madueke da wasu da ake zargi a Najaeriya.

KU KARANTA: Abin da binciken Magu ya ke nufi - Buba Galadima

Jaridar ta ce Magu ya aika wannan martani ne ga kwamitin shugaban kasa wanda ke bincikensa.

Bugu da kari, Magu ya bayyana yadda EFCC ta aikawa hukumomin Birtaniya takarda ta na bukatar a dawo da Alison-Madueke Najeriya a dalilin nawan da aka samu wajen gurfanar da ita.

“A karkashina, EFCC ta samu kyakkyawar alaka da kasar Amurka da hukumar FBI wanda ta yaba da dangatakar da ke tsakaninmu ta hanyar jinjinawa aikin da mu ke yi.” Inji Magu.

Bayan Alison-Madueke, Magu ya ce EFCC ta nemi a dawo da wasu da ake tuhuma da laifi daga kasar waje, amma ofishin AGF ta yi gum da wannan roko da hukumar ta gabatar.

Daga cikin wanda Ministan ya ki bada umarni a taso keyarsu zuwa Najeriya akwai mutumin kasar Amurka, Robert John Oshodin wanda ake zargi da satar kudi a madadin Sambo Dasuki.

Akwai tsofaffin jami’an gwamnatin Jonathan; Kingsley Kuku da Hima Aboubakar da ake zargi da laifin satar dukiyar Neja-Delta, wanda duk ministan bai bada damar maido su gida ba.

Rahoton ya bayyana cewa ofishin ministan bai kai ga magana game da wannan zargi masu nauyi ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel