Saurayi ya bankawa kansa da budurwarsa wuta bayan ya malale dakinsu da fetur

Saurayi ya bankawa kansa da budurwarsa wuta bayan ya malale dakinsu da fetur

- Hankulan jama'a sun tashi a yankin unguwar Inikpi da ke Makurdi a jihar Benuwe bayan wani mutum ya kone kansa tare da budurwarsa

- Mutumin, wanda ba'a kai ga gano ko waye ba zuwa yanzu, ya mamale dakinsu da fetur kafin daga bisani ya cinna wuta

- Mutumin mai kimanin shekaru arba'in ya mutu sanadiyyar gobarar, inda ita ma buduruwar tasa ta ƙone fiye da tsammani

Wannan abun al'ajabi mai kama da almara ya afku a birnin Makurdi,jihar Benue inda wani mutum mai matsaikatan shekaru ya cinnawa kansa da budurwarsa wuta.

Bayanai sun nuna cewa mutumin wanda har zuwa lokacin tattara wannan rahoton ba'a kai da gano kowaye ba, ya siyo fetur, ya kulle kansa a ɗaki tare da buduruwarsa a ciki kafin ya banka musu wuta gabaki ɗayansu.

Mutumin mai kimanin shekaru arba'in ya mutu sanadiyyar gobarar, inda ita ma buduruwar tasa ta ƙone fiye da tsammani.

Wannan lamari ya faru a ƙarshen titin Inikpi, wata babbar unguwa a Makurɗi, da yammacin ranar Asabar da misalin ƙarfe shida da rabi 6:30pm.

KARANTA: Na baka wa'adin mako guda ka saki matarka ka aure ni; Farka ta umarci dadironta

Lokacin da jaridar The Nation suka ziyarci Ofishin Hukumar kiyaye afkuwar haɗari(FRSC) sun ga lokacin da ake fitar da gawar mutumin da kuma buduruwarsa zuwa asibiti.

Saurayi ya bankawa kansa da budurwarsa wuta bayan ya malale dakinsu da fetur
Saurayi ya bankawa kansa da budurwarsa wuta bayan ya malale dakinsu da fetur
Asali: Getty Images

A wani labarin mai nasaba da wannan da Legit.ng Hausa ta wallafa, wani matashin yaro ya harbe iyayensa da ƴan'uwansa ƙanana guda 3 har lahira bayan ya gano cewa wadda ya ɗauka a mahaifiyarsa kishiyar uwarsa ce da ta rike shi.

Sai dai kuma duk da ya kashe 'yan uwansa yaron ko kaɗan bai nuna nadamarsa ba.

A yanzu haka yaron mai suna Masom Sisk, ya na da shekaru 15 a duniya.

Wanda ake zargi da kisan kiyashin kwata-kwata bai nuna damuwa a kan irin ɓarnar da ya aikata ba. Ana zarginsa da laifin ne a kotun yara ta Limestone County,Alabama,a watan Satumbar 2019.

Shugaban sashen wa'adin gyara hali na ɓangaren yara a Limestone County,Jami'i Tara Pressnell yace;.

KARANTA: Sabuwar doka: Ma su digiri mai daraja ta farko da ta biyu kadai za'a bawa aikin koyarwa; FG

"Sisk bai nuna wata alamar damuwa ko nadama a bisa laifin da ake tuhumarsa na kashe iyalansa ba. Lokacin da ake tsare dashi bai taɓa hira ko magana akan iyalinsa ba ko kaɗan."

Matashin bai nuna kaico da nadamar aikita laifin da yayi ba. Ana tuhumarsa ne yi a matsayin baligi da laifin kashe rayuka biyar murus har lahira.

An ce ya yi harbe-harben ne jim kaɗan bayan ya gano cewar Mary Sisk, ƴar shekara 35, ba ita ce uwar data haife shi ba, duk da har yanzu masu bincike basu tabbatar da batun ba.

Ana zargin Sisk da kashe mahaifinsa John Sisk,mai shekara 38, Kishiyar babarsa Mary Sisk, mai shekaru 35, ɗan uwansa, Grayson, mai shekaru 6, ƴar uwarsa; Aurora, mai shekaru biyar, da kuma ɗan uwansa jinjiri ɗan wata shida mai suna Colson a gidansu dake Elkmont.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng