Lekki: Ba mu yi amfani da harsashin gaske a kan masu zanga-zanga ba; rundunar soji ga magantu

Lekki: Ba mu yi amfani da harsashin gaske a kan masu zanga-zanga ba; rundunar soji ga magantu

- A karshe, rundunar soji ta tura wakilci domin wanke kanta daga zargin budewa fararen hula wuta a Lekki, jihar Legas

- Kwamandan barikin soji ta 81 da ke Victoria Island a jihar Legas, Birgediya Janar Ahmed Taiwo, ne ya wakilci rundunar soji

- Birgediya Janar Taiwo ya nuna faifan bidiyon abinda ya faru a majigi domin mambobin kwamitin su ganewa idonsu

Rundunar soji, a ranar Asabar, ta musanta zargin yin amfani da harsashin gaske a kan fararen hula da suka yi dandazo a Lekki, jihar Legas, yayin da suke gudanar da zanga-zangar neman a rushe rundunar SARS; wato ENDSARS.

Birggediya Janar Ahmed Taiwo, kwamandan barikin soji ta 81 da ke Vitoria Island a Legas, ne ya fadi hakan yayin da ya wakilci hedikwatar rundunar tsaro a gaban kwamitin bincike da gwamnatin jihar Legas ta kafa.

A cewar Birgediya Janar Taiwo, dakarun soji sun yi harbi sama da fankon harsashi (harsashin roba) domin tarwatsa masu zanga-zangar.

KARANTA: Matashi ya kashe dukkan mutanen gidansu bayan ya gano shi dan riko ne

A yayin da ya ke jawabi, Birgediya Janar Taiwo ya yi amfani da majigin da ya jona a jikin na'ura mai kwakwalwa wajen nuna faifan bidiyon soji yayin da suka tsaya a gaban masu zanga-zangar suke harba harsashin roba a sama.

Lekki: Ba mu yi amfani da harsashin gaske a kan masu zanga-zanga ba; rundunar soji ta magantu
Lekki: Ba mu yi amfani da harsashin gaske a kan masu zanga-zanga ba; rundunar soji ta magantu @Channels24
Asali: Twitter

Ya ce za'a samu asarar rayuka da dakarun soji sun yi amfani da alburushi na gaske domin tarwatsa masu zanga-zangar.

"Na shiga aikin soja tun shekarar 1986, a saboda haka, an san ba za a budewa jama'a wuta ba amma su cigaba da rera waka.

KARANTA: Bayan shekara dubu uku, an gano wata siffa a sansanin da sojojin Annabin Dauda suka mamaye a Golan

"Ina da kwarewar sanin harsashi saboda dadewa a cikin ikin soja, harsashin roba bashi da sauri kamar na gaske, ba ya ratsa tsokar jikin mutum, ba ya illa matukar ba kusa da mutum aka zo aka harba masa shi a cikin idonsa ba.

"Koda a kusa da fatar jikin aka harbi mutum, sai dai gurin ya yi alamar konewa," a cewarsa.

Birgediya Janar Taiwo, ta hannun lauyan rundunar soji, Mista Akinolu Kehinde, ya mikawa kwamitin irin harsashin da suka yi amfani da shi domin kafa hujja.

A ranar 29 ga watan Oktoba ne Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa Sani Usman Kukasheka, tsohon kakakin rundunar soji, ya ce sojoji sun harba harsashin roba ne, ba na gaske ba, a kan dandazon masu zanga-zanga da suka mamaye yankin Lekki a garin Legas.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel