Ana rade-radin Gwamnan Ebonyi David Umahi zai sauya-sheka a makon nan
- Ana rade-radin Dave Umahi ya fice daga jam’iyyar, ya koma APC
- Rahotanni sun ce Gwamnan Ebonyi zai bayyana haka kwanan nan
- Shugabannin kananan hukumomi za su bi gwamnan zuwa APC
Akwai jita-jita da ke yawo cewa gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya fice daga jam’iyyar PDP, ya kuma zabi ya shiga tafiyar APC mai mulki.
Jaridar Punch ta ce babu mamaki gwamnan ya tabbatar da sauyin-shekarsa a wannan makon.
A ranar Asabar, 17 ga watan Oktoba, rahotanni su ka bazu cewa gwamnan aka zaba a karkashin rigar PDP, ya sauya-sheka zuwa jam’iyyar APC.
KU KARANTA: Mutanen Ibo sun fara shiri da bangaren Arewa saboda zaben 2023
Wani hadimin David Umahi ya karyata wadannan rahotanni a cikin karshen makon da ya gabata, ya ce mai gidansa ya na nan daram a tafiyar PDP.
Amma wani ‘dan majalisa mai wakiltar mazabun Ezza da Ikwo, Honarabul Chinedu Ogah ya tabbatarwa ‘yan jarida cewa gwamnan ya bar PDP.
Chinedu Ogah ya ce gwamnan ya kalubalanci masu karyata jita-jitar, ya ce a fada wa kowa cewa gwamnan jihar Ebonyi, ya koma jam’iyyarsu ta APC.
Ogah mai wakiltar Ezza da Ikwo a karkashin jam’iyyar APC, ya ce gwamnan ya sauya-sheka.
KU KARANTA: Gwamnoni sun yagi N185b a matsayin rabon Satumba - FAAC
“Eh, sauyin-shekar gwamna Umahi zuwa jam’iyyarmu ta APC, abu ne mai kyau. Ba za mu cigaba da zama a adawa ba. Dole mu shiga jam’iyya mai mulki.”
Jaridar ta rahoto ‘dan majalisar ya cigaba da cewa: “Ina kiran sauran gwamnonin Kudu maso gabas, su bi sahun gwamna Umahi, su shigo APC.”
Shugaban kasa (Buhari) ya yi kokari, kowa ya mara masa baya, inji ‘dan siyasar. Ana tunanin duk shugabannin kananan hukumomin jihar za su bar PDP.
Dazu mu ka ji cewa wasu kungiyoyin Matasa sun ba Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari lakanin kawo karshen #EndSARS da yajin-aikin ASUU.
Kungiyar ta ambaci wasu gwamnoni biyu da ya kamata su zauna da shugaban kasa kan lamarin.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng