EndSARS: Kuna da makonni 2 don yin bincike a kan Sam Adeyemi da sauransu, kotu ga yan sanda

EndSARS: Kuna da makonni 2 don yin bincike a kan Sam Adeyemi da sauransu, kotu ga yan sanda

- Rundunar yan sanda a Abuja za ta binciki Sam Adeyemi na cibiyar Daystar Christian Centre, Aisha Yesufu da sauran mutanen da suka daukaka zanga zangar EndSARS

- Wata kotun majistare da ke Abuja ce ta bayar da umurnin binciken

- Ana sanya ran yan sandan za su gudanar da binciken a cikin makonni biyu

Ga dukkan alamu an dauki karar da aka shigar kan wasu mutane da ake kallo a matsayin wadanda suka daukaka zanga zangar EndSARS da muhimmanci domin tabbatar da tsoron yan Najeriya da dama makonni bayan gangamin.

Wata kotun majistare da ke Abuja ta umurci rundunar yan sanda a birnin tarayya da ta binciki lamuran da ake zargin Sam Adeyemi, Aisha Yesufu da sauransu da hannu a ciki.

Kwamishinan yan sandan birnin tarayya, Bala Ciroma aka bai wa umurnin, a ranar Asabar, 14 ga watan Nuwamba, jaridar The Cable ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Zan ci gaba da aure aure har sai na samu wanda ya dace da ni, in ji bazawara mai aure 10

EndSARS: Kuna da makonni 2 don yin bincike a kan Sam Adeyemi da sauransu, kotu ga yan sanda
EndSARS: Kuna da makonni 2 don yin bincike a kan Sam Adeyemi da sauransu, kotu ga yan sanda Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Kotun ta bai wa Ciroma makonni biyu ya kammala bincikensa sannan ya gabatar mata da rahoto kafin ta yanke hukuncinta.

Wasikar kotun ya zo kamar haka:

“Shugaban kotun majistare na II, Hon. Omolola Tolulope Akindele, da ke zama a babbar kotun majistare na 2, Wuse Zone 6, FCT Abuja, ya umurceni da na rubuta wasika zuwa ofishinka domin ka binciki lamarin da aka bayyana a sama sannan ka kawo masa rahoto cikin makonni biyu domin yanke hukuncin da ya kamata.”

KU KARANTA KUMA: Dogarin Gwamna Obaseki ya yanke jiki ya fadi a wajen bikin rantsar da shi (bidiyo)

A baya mun ji cewa an maka yan Najeriya hamsin a bangarori daban-daban da suka hada da mawaki David Adeleke, jagorar #BringBackourGirls, Aisha Yesufu da kuma Fasto Sam Adeyemi a gaban kotun majistare da ke Abuja.

An kai su kotu ne a kan rawar ganin da suka taka a zanga zangar EndSARS da aka yi kwanan nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel