Bidiyo da hotunan ragargazar da soji suka yi wa 'yan bindiga yayin da suke kwashe shanu a Kaduna
- Rundunar OPERATION THUNDER STRIKE, tana cigaba da samun nasara a jihar Kaduna, inda suke ragargazar 'yan bindiga ta jirgin sama
- A ranar 12 ga watan Nuwamban 2020, rundunar sojin saman ga samu nasarar kashe daruruwan 'yan ta'adda, masu dauke da miyagun makamai
- Sun hango 'yan ta'addan suna tafe a babura tare da shanu da tumaki masu yawa daga kauyen Dankolo suna tunkarar dajin kwiambana
Rundunar sojin sama ta Operation Thunder Strike ta samu nasarar kashe wasu 'yan ta'adda da suke dauke da miyagun makamai.
'Yan ta'addan suna tafe ne a babura tare da shanu da tumakai a kauyukan Dankolo da Machitta da ke jihar Kaduna.
Rundunar sojin saman sun hangi 'yan ta'addan ta wata na'ura mai hangen nesa, inda suka hangi 'yan ta'addan a kauyen Kaboru, suna tunkarar dajin Kwiambana.
Kakakin rundunar sojin, John Enenche, ya sanar da hakan a wata takarda, wacce yace rundunar Operation THUNDER STRIKE ta ragargaji mafi yawan 'yan bindigan da ke dajin Kwiambana a jihar Kaduna.
Kamar yadda yace, "Ragargazar ta auku ne a ranar 12 ga watan Nuwamba 2020, inda rundunar sojin saman ta samu nasarar kashe daruruwan 'yan ta'addan da ke dauke da miyagun makamai suna tafe a babura da shanaye da tumaki masu yawan gaske, daga kauyen Dankolo suna tunkarar kauyen machitta."
KU KARANTA: A karon farko, Tinubu ya magantu a kan daina biyan tsoffin gwamnonin Legas fansho
KU KARANTA: 'Yan jihar Kaduna za su fara biyan harajin 1,000 a kowacce shekara, KADIRS
A wani labari na daban, hukumar 'yan sanda ta jihar Legas ta bayyana korar jami'an 'yan sanda guda 10 a ranar Laraba da tayi, saboda sun aikata laifuka daban-daban.
Kakakin hukumar, SP Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana hakan a wata takarda da ya sa hannu, kuma ya gabatar wa manema labarai a jihar Legas.
Kamar yadda kakakin yace, anyi korar ne don ladabtar da 'yan sandar jihar, Daily Nigerian ta wallafa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng