Harsashin roba sojoji suka yi amfani da shi a kan masu zanga-zanga - Kukasheka

Harsashin roba sojoji suka yi amfani da shi a kan masu zanga-zanga - Kukasheka

- Har yanzu batun zargin dakarun soji da budewa masu zanga-zanga wuta a Lekki, jihar Legas, bai daina daukan hankali ba

- An samu mabanbantan rahotanni a tsakanin gwamnati da kafafen yada labarai a kan gaskiyar abinda ya faru a Lekki

- Tuni gwamnatin jihar Legas ta kafa kwamitin bincike da zai zakulo hakikanin gaskiyar abin da ya wakana a Lekki

Sani Usman Kukasheka, tsohon kakakin rundunar soji, ya ce sojoji sun harba harsashin roba ne, ba na gaske ba, a kan dandazon masu zanga-zanga da suka mamaye yankin Lekki a garin Legas.

Kafafen yada labarai da dama, a gida da ketare, sun wallafa rahotannin cewa sojojin Najeriya sun budewa fararen hula masu zanga-zanga wuta a Lekki.

Sai dai, gwamnatin Najeriya ta musanta rahotannin tare da kafa kwamitin bincike da zai bankado gaskiyar abinda ya faru a Lekki.

KARANTA: Sabon hari a Katsina: Yan bindiga sun sace mata uku yayin artabu da 'yan sanda

Da ya ke magana a wani shirin gidan Talabijin din 'Arise' a ranar Alhamis, Kukasheka; birgediya janar mai ritaya, ya ce harsashin roba ba ya kisa, a saboda haka babu gaskiya a rahotannin da ke cewa an rasa rayuka a Lekki.

Yayin tattaunawar da aka yi da shi, Kukasheka ya ce akwai dalilai masu karfi da suka tilasta gwamnati yin amfani da sojoji a kan masu zanga-zanga.

Harsashin roba sojoji suka yi amfani da shi a kan masu zanga-zanga - Kukasheka
SU Kukasheka mai ritaya @TheCable
Asali: Twitter

A cewarsa, wasu kungiyoyi na gida da ketare sun fara saka jari a zanga-zangar, lamarin da ya haddasa barkewar rikici a sassan Najeriya, wanda kuma hakan ne yasa gwamnati yin amfani da sojoji.

KARANTA: Abuja-Kaduna: Masu garkuwa sun kashe Kanal a rundunar soji bayan karbar kudin fansa N10m

"Tabbas, an tura sojoji, amma kwamitin bincike zai gano silar dalilin tura sojoji da abin da ya faru bayan isarsu wurin.

"Za mu bar kwamitin bincike ya yi aikinsa, amma jama'a su sani cewa sojoji sun harba harsashin roba ne, wanda ba ya kisa koda kuwa an harbi mutum a kusa ne.

"Akwai matukar hatsari jama'a suke saka siyasa a batun tsaron kasa. Bai kamata a yi kokarin kawo siyasa da raba kan rundunar soji ba," a cewar Kukasheka.

Masu zanga-zangar EndSARs sun zarce da kashe-kashe tare da kone-kone wanda ya koma tarzoma

Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya ce ko nan gaba Najeriya ta tarwatse, toh babu shakka kiyayya ce ta tarwatsa ta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng