Bayan shekara dubu uku, an gano wata siffa a sansanin da sojojin Annabin Dauda suka mamaye a Golan

Bayan shekara dubu uku, an gano wata siffa a sansanin da sojojin Annabin Dauda suka mamaye a Golan

- Bayan kimanin shekaru dubu uku, an gano wani sansani a kasar Isra'ila mai alaka da Annabi Dauda

- Masana kimiyyar tarihi sun bayyana cewa sun gano wata ƙerarriyar siffa dake nan tun zamanin Annabi Dauda

- Duk da Annabi Dauda (King David) ya kasance mabiyin addinin Juda, tarihinsa ya zo a Injila da Qur'ani

Masana kimiyyar tarihi a ranar laraba sun gano wata ƙerarriyar siffa da ke nan tun zamanin Annabi Dauda wadda ke ƙarin haske game da iyakokin haɗakar littafi mai girma na injila da Isra'ila.

Sansanin mai kimanin shekaru dubu uku, an gano shine a mazaunin Yahudawan Hispin a ƙokarin aikin gina sabon wuri da zai maƙwabtaka da wurin, an yarda cewa mallakin masaurautar Geshur na mabiya sarki David ne.

An gano wata sassaƙar hannu a jikin dutse mai kyalli wadda ta fito ɓaro ɓaro aƙalla tsawon ƙafa biyar a jikin saman tsauni.

Barak Tzin, wanda ya bada umarnin haƙa rami, ya yi ƙiyasin cewa ramin ya kai tsayin 1,000sq, kwatankwacin ɗaya bisa huɗu na eka.

KARANTA: Buhari ya amince da gina sabbin cibiyoyin nazari da bincike 12 a Nigeria

Mahaƙan sun gano ƙaton dutse wanda akayi sassaƙa mai ɗauke da zanen ƙaho biyu da kuma gunkin wata mata ta riƙe na'urar sautin kiɗa wacce ta fi kama da ganga.

"Hakan yasa mun alaƙanta da shekarar ƙarafa," a cewar Tzin.

Ya kara da cewa; ''mu na da masaniyar samun makamancin irin wannan tarihin a Bethsaida, wani ɓangare mai alaka da birnin masaurautar Geshur" wacce ta ke yammacin Hispin a arewacin gaɓar tekun Galilee.

Bayan shekara dubu uku, an gano wata siffa a sansanin da sojojin Annabin Dauda suka mamaye a Golan
Bayan shekara dubu uku, an gano wata siffa a sansanin da sojojin Annabin Dauda suka mamaye a Golan @Vanguard
Asali: Twitter

Tzin ya ce akwai alamar da ke nuna cewa akwai alaƙar dangi tsakanin masarautar Geshur da masarautar David.

''Badalar sansanin Hispin ita ce irinta ta farko da aka gano, ta ƙara sarƙaƙiya ga masana tarihin kimiyya,'' acewar Tzin.

KARANTA: Dalilin da yasa na sace ɗalibata ƴar shekara takwas; Matashin Malami

''Wannan abin mamakin zai iya ƙara faɗaɗa fiye da sanin mu. Binciken Golan har yanzu bai kai ƙololuwa ba, mun fara gano Golan ne yanzu"

''Mutanen nan gaba zasu iya bayyana mana iyakar Geshuwar da lokacin da sansani Hispin zai gama ɓullowa,'' a cewarsa.

"Mun yarda cewa fadar ta watsu har Syria.Ya cike gurbin da ke tsakani," ya bayyana hakan loƙacin da yake Hispin.

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa a farkon watan Oktoba, Fafaroma Francis, jagoran mabiya addinin Kirista a duniya, ya ce shugaban kasar Amurka, "Donald Trump ba kirista bane."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel