Hadimin Saraki ya yi martani kan dakatar da albashin tsofaffin gwamnoni

Hadimin Saraki ya yi martani kan dakatar da albashin tsofaffin gwamnoni

- Matakin na zuwa ne biyo bayan daukar irin matakin da Jihar Legas tace zata yi

- Mai magana da yawun Saraki ya ce wata 33 kenan da tsohon gwamna Abdulfatah Ahmed ya dakatar da biyan fansho ga tsofaffin gwamnoni

- Ya bukaci gwamnati ta dinga bincike kafin ta kwaikwayo wata jihar don kauracewa abin kunya

Wani hadimin tsohon gwamnan Kwara, Bukola Saraki, ya soki gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, kan wani alkawarin karya dokar da ta tabbatar da biyan tsofaffin gwamnoni fansho tsahon rayuwarsu dama wasu hakkoki su da mataimakansu.

Abdulrazaq ya yi alkawarin yin watsi da dokar biyan fanshon kwanaki kadan bayan gwamnan Lagos, Babajide Sanwa-Olu, ya yi alkawarin mika kudirin gaban majalisa akan irin wannan doka a jihar.

Sai dai, Abdulganiyu Abdulqadir, mai magana da yawun Saraki, a harkokin cikin gida, ya ce an karya dokar tun 2018 kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Hadimin Saraki yayi martani kan dakatar da albashin tsofaffin gwamnoni
Hadimin Saraki yayi martani kan dakatar da albashin tsofaffin gwamnoni. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hadimin Ganduje ya rabawa matasa tallafin jakuna a Kano (Hotuna)

A wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a, Abdulqadir ya shawarci gwamnatin Jihar Kwara da ta dinga bincike kan al'amura kafin kwaikwayo wata jihar don kauracewa abin kunya.

Ya ce tsohon gwamna Abdulfatah Ahmed ya dakatar da biyan fansho ga tsofaffin gwamnoni da mataimakansu tun watan Fabarairun 2018, watanni 33 da suka gabata.

Abdulqadir ya ce, "abin damuwa ne yadda aka shigo da siyasa cikin hukuncin da gwamnati karkashin jagorancin Abdulrahman Abdulrazaq kuma ya zama babban abin da ake batu a tsakanin yan siyasa, ba tare da la'akari da irin abun kunyar da zai janyo al'ummar jihar ba.

"Idan za a iya tunawa a Fabrairun 2018, majalisar dokokin jihar Kwara ta yi wa dokar kwaskwarima kuma ta rushe biyan tsofaffin gwamnoni fansho, abin da ya samu yabo daga shugaban majalisar dattawa na waccan lokacin, Dr Bukola Saraki."

KU KARANTA: Cibiyar Lafiya ta ce ana fuskantar karancin kororon roba a wani gari a Bauchi

Abdulrazaq ya bayyana a ranar Juma'a cewa zai dauki mataki akan dokar da ta baiwa tsofaffin gwamnoni da mataimakansu damar samun fansho a Jihar.

Abdulrazaq, ta bakin Sakataren watsa labarai, Rafiu Ajakaye, ranar Juma'a, ya ce zai mika kuduri a gaban majalisa don warware dokar.

A wani labarin, Gwamnan Ebonyi, Dave Umahi, ya gaya wa shugabancin jam'iyyar PDP a Abuja ranar Talata cewa zai bar jam'iyyar.

Ya ce zai koma jam'iyya mai mulki ta APC yana mai ikirarin cewa APCn zata bawa dan yankin sa na kudu maso gabas takara a zaben 2023.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel