Cibiyar Lafiya ta ce ana fuskantar karancin kororon roba a wani gari a Bauchi

Cibiyar Lafiya ta ce ana fuskantar karancin kororon roba a wani gari a Bauchi

- Magidanta a Kafin Madaki da ke karamar hukumar Ganjuwa na Jihar Bauchi sun koka game da karancin kayan bada tazarar haihuwa ciki har da kororon roba

- Shugaban Kwamiti na Cigaban Cibiyar Lafiya ta Kafin Madaki, Mustapha Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin jawabin da ya yi da 'yan jarida

- Shugaban cibiyar lafiyar ya ce sunyi nasarar wayar da kan magidanta sun fahimci muhimmancin bada tazarar haihuwa musamman a mawuyacin halin da tattalin arzikin kasa ke ciki

Wasu magidanta a karamar hukumar Ganjuwa ta Jihar Bauchi sun koka kan karancin kororon roba a yankin wadda ke taimaka musu wurin bada tazarar haihuwa.

The Punch ta ruwaito cewa shugaban kwamitin Cibiyar Lafiya ta mazabar Kafin Madaki, Mustapha Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin da ya yi wa manema labarai jawabi.

An koka kan rashin isasun kororon roba a wani gari a Bauchi
An koka kan rashin isasun kororon roba a wani gari a Bauchi. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Wanda ya yi ƙarar Rahama Sadau ya ce fadar shugaban kasa da wani kwamishinan 'yan sanda ke hana a kama ta

"Mu a matsayinmu na kwamiti, mun dukufa wurin wayar da kan al'umma kuma da dama cikinsu sun rungumi wannan tsarin sosai.

"Maza a yanzu suna fitowa fili su nemi a kawo musu kororon roba don su taimakawa matansu, sai dai a halin yanzu wadanda muke da su nan sun kare," a cewarsa.

Ya cigaba da cewa, maza sun fara fahimtar cewa bada tazarar haihuwa yana da matukar muhimmanci musamman idan aka yi la'akari da irin halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.

KU KARANTA: Hotuna: Za a birne wani hamshaƙin attajiri tare da sunƙin daloli

Ibrahim ya mika rokonsa ga Cibiyar Lafiya Bai Daya na Jihar Bauchi ta taimaka ta samar musu da kayayyakin bada tazarar haihuwa ciki har da kororon roba ta yadda mazauna garin za su iya amfana da shi.

Mataimakin shugaban Cibiyar, Kafin Madaki, Sani Usman yayin jawabi kan ayyukan da cibiyar lafiyar ke yi ya ce, sun samu a kalla mutane 58 da ke neman bada tazarar haihuwa a cikin watan Oktoban 2020.

Sai dai ya ce a watan Nuwamba da muke ciki a yanzu cibiyar ta samu karancin kayayyakin taimakawa wurin bada tazarar haihuwa.

A wani labarin, abokan wani attajirin Zimbabwe, Genius Kadungare wanda yafi shahara da Ginimbi a fagen zamantakewa sunce za a binne shi ne da tarin daloli, wata majiya ta kusa ta ruwaito.

Dan kasuwar wanda ya yi rayuwa ta alfarma, shine ya bar wasiyar, a cewar jaridar Herald.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel