Da duminsa: An kashe mataimakin kwamandan Al-Qaeda
- Wani rahoto ya bayyana cewa an kashe mataimakin Kwamandan Al-Qeada bisa umarnin Amurka a Tehran
- Ana zargin Abdullah da tarwatsa ofisoshin jakadancin Amurka a Tanzaniya da Kenya a shekarar 1998
- Hukumar yaki da ta'addanci ta kasar Amurka ta ce baya hannun hukumomin Kasar kuma gwamnati ta sanya tukuici ga duk wanda ya bada bayani kan yadda za a gano shi
Mataimakin babban kwamandan Al-Qeada da aka gurfanar a Amurka a kan tarwatsa musu ofisoshin jakadanci a Tanzaniya da Kenya a shekarar 1998, rahotanni daga jaridar New York Times ta ruwaito ranar Juma'a cewa an kashe shi a sirrance tun cikin watan Agusta.
Abdullah Ahmed Abdullah wanda ke cikin jerin wanda rundunar FBI ke nema ruwa a jallo, an harbe shi kuma ya mutu a Tehran daga wasu jami'an Isra'ila a bisa umarnin Amurka, jami'ai na musamman sun tabbatar wa jaridar times.
DUBA WANNAN: Gobara ta tashi a ofishin hukumar wutar lantarki na garin Jos
Amurka, Iran, Isra'ila, ko Al-Qeada basu dauki alhakin harin da ya faru a ranar 7 ga watan Agusta lokacin tunawa da ranar fashewar bama-baman Afirka, The Punch ta ruwaito.
Babban shugaban Al-Qeada, Abu Muhammad Al-Masri, an kashe shi tare da ýar sa Miriam, tsohuwar matar Osama bin Laden, a rahoton jaridar Times.

Asali: Twitter
Gwamnatin Amurka ta sanya ladan dala miliyan 10 ga duk wanda ya bada wani bayani da zai yi sanadiyar kama shi.
DUBA WANNAN: Kansila ya yi wa matar yayansa mugun duka bayan zarginta da maita
Abdullah shine "mafi wayo da kwarewa wajen tsara hare-hare, baya hannun Amurka ko kuma a hannun hukumomin ta", kamar yadda yake a wata takarda ta hukumar yaki da ayyukan ta'addanci Amurka ta fitar a 2008, a cewar jaridar Times.
Tarwatsa ofisoshin jakadancin a Kenya da Tanzaniya a shekarar 1998 ya janyo mutuwar mutane 224 da kuma raunata fiye da mutane 5,000.
An gurfanar da Abdullah a gaban babbar kotun tarayya a Amurka sakamakon laifin.
A wani labari na daban, Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz Al Saud ya kira Shuguba Muhammadu Buhari na Najeriya a wayar tarho, a ranar Alhamis kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Saudiyya ya ruwaito.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng