Sarkin Saudiyya ya kira Buhari ta waya sun tattauna
- Sarki Salman bin Abdulaziz na kasar Saudiyya ya kira Shugaba Muhammadu Buhari ta wayar tarho
- Shugabannin biyu sun tattauna kan batutuwan da suka shafe kawancen diflomasiyya tsakanin kasashen biyu
- Ko a watan Agusta, Sarki Salman ya kira Shugaba Buhari ta waya inda nan ma suka tattauna kan farashin man fetur na duniya
Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz Al Saud ya kira Shuguba Muhammadu Buhari na Najeriya a wayar tarho, a ranar Alhamis kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Saudiyya ya ruwaito.
DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya, sun sace wasu da dama a hanyar Kaduna zuwa Abuja
Shugabanin biyun sun tattauna batutuwa ne masu alaka da kawancen diflomasiyya da ke tsakaninsu da hanyoyin da za a bi don inganta yarjejeniyar da ke tsakanin kasashen biyu a cewar Saudi Gazette.
Wannan shine karo na biyu da sarkin na Saudiyya ke kiran Buhari ta waya.
KU KARANTA: Gwamnan Jihar Zamfara ya rattaba hannu kan wasu dokoki huɗu masu muhimmanci
A baya cikin watan Agusta, Sarki Salman ya kira don tattaunawa kan hanyoyin da za a daidaita farashin man fetur a kasuwannin duniya.
A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, wasu magidanta a karamar hukumar Ganjuwa ta Jihar Bauchi sun koka kan karancin kororon roba a yankin wadda ke taimaka musu wurin bada tazarar haihuwa.
The Punch ta ruwaito cewa shugaban kwamitin Cibiyar Lafiya ta mazabar Kafin Madaki, Mustapha Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin da ya yi wa manema labarai jawabi.
"Mu a matsayinmu na kwamiti, mun dukufa wurin wayar da kan al'umma kuma da dama cikinsu sun rungumi wannan tsarin sosai.
"Maza a yanzu suna fitowa fili su nemi a kawo musu kororon roba don su taimakawa matansu, sai dai a halin yanzu wadanda muke da su nan sun kare," a cewarsa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng