Gobara ta tashi a ofishin hukumar wutar lantarki na garin Jos

Gobara ta tashi a ofishin hukumar wutar lantarki na garin Jos

- An yi gobara a ofishin hukumar samar da wutar lantarki na garin Jos a jihar Plateau

- Goboran ya fara ci ne misalin karfe shida na yammacin ranar Juma'a a hedkwatar hukumar da ke Ahmadu Bello Way

- Mai magana da yawun kamfanin ya ce jami'an kwana kwana sun hallara kuma suna kokarin kashe wutar

Hedkwatar hukumar samar da wutar lantarki na Jos da ke kan titin Ahmadu Bello Way, Jos, ta kama da wuta a ranar Juma'a 13 ga watan Nuwamban 2020.

Sakamakon gobarar, sassa da dama na garin na zaune cikin duhu.

An gano cewa wutar ta fara ne daga hawa na hudu na ginin misalin karfe 6 na yamma.

Gobara ta tashi a ofishin hukumar wutar lantarki na Jos
Gobara ta tashi a ofishin hukumar wutar lantarki na Jos. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 2023: Zan fice daga PDP zuwa APC, in ji Gwamnan Ebonyi

Shugaban sashin hulda da jama'a na kamfanin, Dakta Adakole Elijah ya tabbatar da faruwar lamarin a wayar tarho da suka yi da The Punch.

Elijah ya ce, "Eh, da gaske ne. Babban ofishin mu na Jos ya yi gobara amma an sanar da jami'an hukumar kwana kwana na Jos kuma suna kokarin kashe wutar."

KU KARANTA: Wasu mazauna Kaduna sun soki harajin cigaba na N1,000 da gwamnati ta sakawa duk baligai

Ba a samu asarar rai ba kawo yanzu.

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, wasu magidanta a karamar hukumar Ganjuwa ta Jihar Bauchi sun koka kan karancin kororon roba a yankin wadda ke taimaka musu wurin bada tazarar haihuwa.

The Punch ta ruwaito cewa shugaban kwamitin Cibiyar Lafiya ta mazabar Kafin Madaki, Mustapha Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin da ya yi wa manema labarai jawabi.

"Mu a matsayinmu na kwamiti, mun dukufa wurin wayar da kan al'umma kuma da dama cikinsu sun rungumi wannan tsarin sosai.

"Maza a yanzu suna fitowa fili su nemi a kawo musu kororon roba don su taimakawa matansu, sai dai a halin yanzu wadanda muke da su nan sun kare," a cewarsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel