Jami'an kwastam sun bude wa fusatattun matasa wuta a Kebbi, mutum daya ya mutu

Jami'an kwastam sun bude wa fusatattun matasa wuta a Kebbi, mutum daya ya mutu

- An samu rashin jituwa tsakanin matasa a Jihar Kebbi da jami'an hukumar Kwastam hanyar Kamba zuwa Bunza

- Matasan sun yi yunkurin fito na fito da jami'an na kwastam a yayin da suka kama wata mota dauke da shinkafar kasar waje

- Daya daga cikin jami'an kwastam ya harbi matashi daya wadda daga bisani ya rasu bayan an kai shi asibiti

Tawagar jami'an hukumar kwastam ta Zone B, Kaduna da ke aiki a titin Kamba/Bunza sun harbi wasu matasa da ke zanga zanga inda suka kashe guda suka raunata wasu da dama kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Sai dai, sanarwar da kakakin hukumar ya fitar a ranar Alhamis, Ma Magaji, ya ce matasan sun kai wa jami'an hari ne bayan sun tare wani mota dauke da buhunnan shinkafar kasar waje da ake zargin an shigo da ita ta haramtaciyyar hanya.

Jami'an kwastam sun bude wa fusatattun matasa wuta a Kebbi, mutum daya ya mutu
Jami'an kwastam sun bude wa fusatattun matasa wuta a Kebbi, mutum daya ya mutu. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Cibiyar Lafiya ta ce ana fuskantar karancin kororon roba a wani gari a Bauchi

A cewar sanarwa, matasan da ke dauke da muggan makamai sun yi yunkurin karbe bindigar daya daga cikin jami'an ne.

"Sakamakon hakan, aka yi harbin bindiga wacce kuma harsashin ta samu daya daga cikin matasan a kafadarsa.

"An garzaya da matashin da ya raunata zuwa babban asibitin Kamba nan take, yayin da wasu daga cikin jami'an suka samu rauni. Daga bisani matashin ya rasu a asibitin," in ji shi.

KU KARANTA: Hotuna: Za a birne wani hamshaƙin attajiri tare da sunƙin daloli

Sanarwar ta cigaba da cewa hadakar jami'an tsaro sun dakile harin da wasu fusatattun matasa suka kawo daga baya na yunkuri kona barikin kwastam da ke Kamba.

A bangarensa, Kwantrolla, Sarkin Kebbi, yayin yi wa iyalan matashin da ya rasu ta'aziyya ya nuna rashin jin dadinsa game da rasa ran da aka yi.

Kazalika, ya kuma gargadi matasan su guji yin fito na fito da jami'an tsaro da ke gudanar da aikinsu da doka ta tanadar musu.

A wani labarin, wasu ƴan bindiga sun sace hakimin garin Matseri na da ke ƙaramar hukumar Anka a Zamfara, Alhaji Halilu Matseri da yaransa huɗu.

Sun kuma kashe wani Maigaiya Matseri da ya yi ƙoƙarin ceto hakimin kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel